Header Ads

Birnin kebbi-Wani Addu'a don Buhari

A yau Juma'a 24/2/2017 da safe a babban Masallacin Idi da ke anguwar Gesse da ke gari Birnin kebbi,mai girma Gwamnan jihar Kebbi Alh.Atiku Baguda da tawagar sa ciki har da mataimakin Gwamna Samaila Dabai Yombe da sauran jami'an Gwamnati har da mai martaba Sarkin Gwandu,sun jagoranci Sallah da Addu'ar Allah ya kawo sauki wa shugaba Buhari.

Wannan al'amarin ya bani mamaki,tabbas shugaba Buhari yana bukatar addu'a daga 'yan Najeriya musamman Musulmai 'yan Arewacin Najeriya.Duk da yake a jiya 23/2/2017 wasu bayin Allah sun gabatar da irin wannan Addu'a a daidai Masallacin idi wajen da aka gabatar da na yau.Tau me ke faruwa?...Addu'ar na jiya daban ne da na yau?...ko kuma babu wakilci ne a cikin tsarin tafiyar da wannan  Addu'a?

Na tuna bara,lokacin da aka kashe wata baiwar Allah a anguwar bayan Kara da ke nan garin Birnin kebbi,harma akofar gidan Mai martaba Sarkin Gwandu aka yi jana'izan wannan Matar da yara hudu da aka kashe,bayan an sassare matar guntu-guntu kamar yadda muka ji labari.Al'umma Musulmi basu yi irin wannan taron ba domin rokon Allah ya tona asirin wadanda suka aikata wannan aiki.

Kafin wannan lamarin,akwai jita-jita cewa an kuma kashe wani bawan Allah a anguwar Rafin Atiku da ke nan garin Birnin kebbi duk a bara,amma dukkannin wadannan kashe kashen ba a kama kowa ba,amma al'umma sun kasa tunawa cewa ai za'a iya rokon Allah ta salon yadda aka roke shi don Buhari ya sami lafiya.

Allah ya kawo sauki,ya ba da zaman lafiya a jihar Kebbi da Najeriya,Allah ka ba shugaba Buhari lafiya da mu da Gwamnan Jihar Kebbi da Sarakunan mu,da kuma Al'umma Musulmi gaba daya.

Isyaku Garba-Birnin kebbi
@ISYAKUWEB
Powered by Blogger.