Wannan dai na zuwa ne kimanin makwanni biyu da kai hari jami'ar Maidugurin, inda mutane hudu suka rasa rayukansu ciki har da wani Farfesa.
Wani jami'in bayar da agaji ya shaida wa BBC cewar macen farko yt yi hakon gidan wani dan banga ne wanda aka sani da yin bincike a kan motoci a manyan hanyoyin garin.
Sai 'yar kunar bakin waken ta kwankwasa kofar gidan dan bangar, wanda rahotannin suka ce ya ki bude kofar.
Saboda haka sai ta yi maza ta rungumi wani mutum da ke kan hanyarsa ta zauwa masallaci kuma ta tayar da bam din da ta yi damara da shi.
Dukkansu biyu sun mutu a harin.
Amma mutumin da ya kai hari na biyun bai samu ya kai ga babban masallacin anguwar Kaleri ba saboda an hanashi zuwa wurin.
Ya mutu shi kadai tare da raunata mutane biyu.
BBCHausa
Tags:
LABARI