Warin Kaji Na Iya Korar Jinsin Sauro Mai Sanya Cutar Maleriya

Ga al'ummar dake zaune a kasashen bakar fata na Afirka, kwanciya ko yin barci a kusa da ibnda kaji suke ba wani bakon abu ba ne, musamman a yankunan karkara.
Masana sun gano cewa akwai jinsunan sauro da dama wadanda sun tsani warin kaji, abinda ke nufin cewa watakila za a iya samo wata hanya mai sauki da arha ta yin rigakafin cutar maleriya da sauron ke haddasawa.
Akasarin sauro, ciki har da wadanda ke dauke da kwayar cutar maleriya, su na cizon mutane, su sanya musu cutar ta hanyar zuba musu jinin da suka dauko mai dauke da kwayar cutar.
Amma ba mutane kawai sauron suke cizo ba, su na cizon shanu, awaki da raguna. Amma kuma ba kowace irin dabba suke cizo ba, kamar yadda masu bincike na kasar Sweden suka gano.
Masanan sun kafa tarakka domin kama sauro a wasu gidaje guda 11 a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia, domin neman wani jinsin sauro da ya fi yawa a wurin, watau Anopheles arabiensis.
Daga nan sai masanan suka gwada jinin dake jikin wadannan sauro, inda suka gano jinin dabbobi da yawa, amma kusan dabbar da babu jininta a jikinsu ita ce kaza, duk da cewa kaji su na da yawa a wurin.
Daga nan sai wani farfesa mai suna Rickert Ignell na Jami'ar Kimiyyar Aikin Gona ta kasar Sweden ya roki mutane 11 a wadannan gidaje 11 da su rika kwana a cikin gidan sauron da ba a sanya masa wani magani ba, amma kuma a kusa da shi an sanya wani abu mai warin kaza. A wani gwajin kuma, kazar aka sanya kusa da gidan sauron.
Masanan sun yi mamaki da suka ga cewa yawan sauron da suka kama a wannan wurin ya ragu da kashi 95 cikin 100 daga wuraren da babu warin kaza ko kuma kaji a kusa.
Yanzu dai masanan suna son su gwada ko za a iya samar da wani abu mai warin kaza da za a rika kunnawa kamar kyandir domin korar sauro daga gidaje.
An wallafa sakamakon wannan binciken ne a wata mujalla mai suna "Malaria Journal."
VOA HAUSA

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN