Najeriya na shirin magance karancin lantarki

A Najeriya sakamakon matsalar wutar lantarki da ake fama da ita, gwamnatin tarayya ta ba da kwangilar fadada wata cibiyar samar da wutar lantarki da ke Odogunyon a Ikorodu na jihar Legas.
 An ware kudade Naira miliyan dubu uku da dari biyar domin wannan aiki, kamar dai yadda taron majalisar koli ta kasar da aka gudanar a wannan laraba ya sanar.
Ministan manyan ayyuka, gine-gine da kuma makamashi, Babatunde Raji Fashola, ya bayyana cewa, wannan kwangilar za ta bada damar samar da tiransifomomi da kuma layukan jan wuta, abin da zai taimaka wajen samun wutar lantarki akai akai a yankin.
Fashola ya ce, tun a cikin shekarar 2009 ne aka bada kwangilar fadada cibiyar amma aka yi watsi da ita saboda karancin kudi.
Jama'a da dama a sassan Najeriya na fama da karancin wutar lantarki, lamarin da ke haifar da cikas ga harkokin kasuwancin wasu daga cikinsu.
RFI Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN