KO ME YA SA BOKO HARAM TA KAI HARI JAMI'AR MAIDUGURI A KARO NA FARKO ?

A karon farko kungiyar Boko Haram ta kai harin kunar bakin wake a jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya,
Mayakan Boko Haram sun fara kai hare-haren a jihohin Borno da Yobe da Adamawa shekaru bakwai da suka gabata da ma wasu jihohin irin su Kano da Kaduna da babban birnin tarayya Abuja.
Sun rika kai hare-haren bam kan wuraren taruwar jama'a da dama da suka hada da makarantu da tashoshin mota da wuraren cin abinci.
Sai dai duk da cewa mayakan sun nuna akidarsu ta kin jinin karatun boko, za a iya cewa wannan ne karo na farko da aka kai harin kunar bakin wake jami'ar Maiduguri, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu da suka hada da wani Farafesa na jami'ar.

Me yasa Boko Haram basu taba kai wa jami'ar hari ba sai wannan karon?
Farfesa Khalifa Dikwa wani tsohon malami ne a jami'ar, ya kuma shaida wa BBC cewa matsin lambar da mayakan ke fuskanta daga sojojin Najeriya a dajin Sambisa ce tasa suke neman inda za su huce fushinsu.
''Da yake sojojin sama ba za su kai musu harin kan mai uwa da wabi ba a dajin saboda suna garkuwa da yara da mata, shi yasa suke fitowa da ire-iren yaran da suke garkuwa da su suke sa su yin kunar bakin wake,'' in ji Farfesa Dikwa.
Ya kara da cewa, ''Suna cike da jin takaicin yadda ake samun galaba sosai a kansu, shine suke ganin kamar idan sun kai hari wurare irin su jami'a za su bai wa gwamnati haushi da takaici ne, su kuma nuna mata suna nan da karfinsu.''
''Sai dai maganar gaskiya ita ce ba wani karfi da suke da shi a yanzu duk wannan abin suna yi ne don neman jan hankali da neman suna, don su jawo hankalin duniya cewa har yanzu za su iya kai manyan hare-hare.''

Yaushe Boko Haram ta fara sa mata kai hare-haren kunar bakin wake?
A farko-farkon shekara ta 2014 ne mayakan Boko Haram suka fara sauya salon kai harin kunar bakin wake ta hanyar amfani da 'yan mata wajen kaddamar da hare-haren.
Galibi dai a kan daura musu rigunan ababan fashewar ne a jikinsu, su kan kuma kai harin a wuraren taruwar jama'a don hallakar da su a lokaci guda.
Sabon salon harin kunar bakin wake da mata suka fara yi a Najeriya wani babban abin tashin hankali ne gami da matukar firgitarwa.
Masana da dama dai na ganin cewa ana yin amfani da matan ne domin yin bad-da-bami, ganin ba a cika tsaurara matakan bincike a kansu ba, saboda la'akari da cewar ba sa son tarzoma.
Wasu kuma na ganin hakan ba ya rasa nasaba da yadda ake kallon mata a matsayin masu raunin zuciya, da tausayi da kuma jin kai.
Mutane da dama ne dai suka rasa rayukansu a a ire-iren wadannan hare-haren kunar bakin wake da mata ke kai wa.
An yi ittifakin cewar ba a fara amfani da mata wajen kai harin kunar bakin wake ba har sai da aka yi watanni biyu da sace 'yan matan sakandaren Chibok, lamarin da wasu ke zargin cewa mai yiwuwa ana amfani da wadannan 'yan mata ne don kai hare-haren.
Wadannan hare-haren kunar bakin wake da 'yan matan ke kai wa, sun fara sauya tunanin al'umma ta fuskar mu'amala da mata a kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama'a, musammma wadanda suke lullube jikinsu da hijabi.
Yayin da dai hukumomin Najeriyar ke ikirarin kakkabe mayakan Boko Haram daga mazauninsu a dajin Sambisa, da alamu kungiyar ta kara kaimi na kai hare-haren kunar bakin wake a cikin birnin Maiduguri.

BBCHausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN