Jihar kebbi za ta kashe Billiyan 139 a kasafin kudin 2017

Gwamnan jihar Kebbi Alhaji Atiku Bagudu ya gabatar wa Majalisar dokoki ta Jihar Kebbi bukatar kasafin kudi na fiye da naira Biliyan 139.A cewar sa wannan shekarar Gwamnati za ta mayar da hankali ne kan harkar gona,tallafa wa kananan masana'antu da sana'oi,ilimi,kiwon Lafiya  da sauran su.
Haka zalika Gwamnan ya yi alkawarin cewa kudi zai shiga hannun jama'ar Jihar Kebbi a bana sabo da tsarin da Gwamnatin ta ke kokarin dauka wa don tallafa wa Al'umman Jihar ta Kebbi.Ya kuma kara da cewa Gwamnatin Jihar Kebbi za ta biya dukkannin kudaden Pansho da Garatuti da Gwamnatin da ta gabata ta bari.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN