Direbobin Manyan Motoci daga Arewa Sun Daina Ba Jami'an Tsaro Na Goro

Gamayyar kungiyoyi da suka hada da masu sarrafa kayan gona, direbobin manyanmotoci da fataken shanu dake safara daga arewa maso gabas zuwa kudancin Najeriya sun tsaida shawarar daina baiwa jami’an tsaro abin goro a shingayen manyan hanyoyi biyo bayan taronsu kan abinda suka bayyana musgunawa da takura masu da a keyi.
Mai Magana da yawun gamayyar kungiyoyin shugaban masana’antar sarrafa anfanin gona na Dak Farm And Milling Industry da ke Jos fadar jihar Filato Sir Mohammed Ali ya ce daga cikin kudurorin da suka dauka akwai na ladabtar da duk wani direba da ya baiwa jami’ai cin hanci a shingayen manyan hanyoyi.
Kamata ya yi gwamnatin tarayya ta fito da tsari na bai daya wanda za a amince da shi a duk sassan kasar don maye gurbin tarin kudaden da suke biya wadanda hukumomi da ke kafa irin wadannan shingayen basu mutuntawa don rage musgunawa da suke fuskanta inj sarkin tashar Mubi dake jihar Adamawa Alhaji Usman Mai Nagge.
Ya ce suna biyan kimanin naira dubu ashirin zuwa dubu talatin kan kowace saniya kwatankwacin naira dubu dari biyu da saba’in kowace tirela da ta tashi daga arewa zuwa kudanci a matsayin abin na goro.
Al’amarin ya fi muni ga direbobi da suke dakon kaya daga kudu idan sun shiga jihar Adamawa dalili ma da ya sa direbobin sun gwammace sauke kayan a Yola Fadar jihar Adamawa da kaiwa kai tsaye zuwa Mubi saboda yawan shingaye dake kan hanyar kamar yadda shugaban direbobin tireloli na kasuwar shanu ta kasa da na Mubi Alhaji Bappa Ibrahim ya shaidawa Muryar Amurka.
muryar Amurka ta tuntubi kakakin rundunar soja na Yola manjo Adamu Yahaya ko suna sane da korafin kungiyoyin inda ya ce rundunar bata umurci jami’anta su amshi kudi daga hannun direbobi ba, kana kuma ta sanar da kungiyoyin su kai mata rahoto da zaran hakan ya abku amma kawo yanzu babu wanda ya kawo mata wani koke.
Saurari Karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.
VOA HAUSA

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN