Buhari ya bukaci a mayar da hankali kan aikin gona don canja akalar tattalin arziki

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya da su mai da hankali akan shirin ba da rancen noma na babban bankin kasa domin samar da abinci da kuma taimaka wa shirin Gwamnati na canja akalan tattalin arziki .Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a sakon da ya aika wajen kaddamar da littafi da kuma ba da lambar yabo  da kungiyar ci gaban Masaurautar Gwandu GEDA ta shirya jiya a fadar Sarkin Gwandu da ke garin Birnin Kebbi.
Taron ya sami halartar Ministan Shari'a na kasa Abubakar Malami SAN.Shugaba Buhari ya lura cewa shirin ya samar da ayyukkan yi ga 'yan Najeriya da kuma canja yanayin aikin gona a kasan nan.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN