ZAMA KUSA DA TITI YANA HAIFAR DA CUTAR MANTUWA

Wani bincike ya gano cewa mutanen da ke zaune kusa da titi sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar mantuwa.
A sakamakon Binciken, kimanin kaso 11 cikin 100 na masu fama da cutar mantuwa da ke zaune kamar mita 50 daga babban titi na da alaka da hada-hadar abubuwan hawa.
Wannan bincike an wallafa shi ne a mujallar Lancet ta kasar Birtaniya.
An gudanar da binciken akan mutanen kasar Canada guda miliyan biyu a tsahon shekaru 11, inda aka samu mutane 243,611 dauke da cutar, kuma mafi yawancin su mazauna kusa da titina ne.
Masu binciken sun ce gurbatacciyar iska daga hayakin ababen hawa tare da hayaniyar su na haifar da dakushewar kwakwalwa.
Kimanin mutane miliyan 50 ne dai ke fama da cutar mantuwa a duniya, al’amarin da ya sa masana ke yunkurin gano musabbabin ta.
ALUMMATA

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN