Hukumomin soji a Nigeria sun ce za
su mayar da dajin Sambisa - inda ya kasance sansanin mayakan Boko Haram
tun shekara ta 2013 - wurin atisaye.
A makon jiya ne dai shugaban
kasar, Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa sojojin sun yi nasarar
kwace dajin daga hannun mayakan. Mai magana da yawun rundunar sojin kasa Birgediya-Janar Sani Usman Kukasheka ya shaida wa BBC cewa za a yi hakan ne domin tabbatar da cewa ''wasu miyagun mutane ba su fake a wannan dajin ba.''
Janar Kukasheka ya ce kuma nan gaba kadan za su yi wa 'yan kasar bayanin abubuwan suka tarar a dajin bayan fattatakar mayakan Boko Haram daga sansanoninsu.
BBC HAUSA
Tags:
LABARI