Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta fitar
da wasu sabbin sharudda da ta ce dole ne, duk wani maniyyaci ya cika su
kafin ba shi damar zuwa aikin hajji a Saudiya.
A
cewar shugaban sashin hulda da kafafen yada labaran hukumar, Alhaji Uba
Mana, sharudan za su taimaka wajen kawo karshen samun masu safarar
miyagun kwayoyi da ke shiga cikin maniyatan Najeriya, da kuma aikata
sauran laifuka a yayin aikin hajji.Mana ya ce yanzu tilasne maniyyaci ya gabatar da wani sahihin mutum, da zai tsaya masa kafin ba shi damar zuwa aikin hajji, wadanda suka hada da, limamin masallacin Juma’a da ma’aikacin gwamnati da ke mataki na 12, ko kuma mai mukamin sarautar gargajiya.
RFI HAUSA
Tags:
LABARI