MANYAN KWAMANDODIN SOJIN NAJERIYA ZA SU YI BIKIN KIRSIMETI A BORNO

Rundunar sojin Najeriya ta umurci manyan kwamandojinta, su tafi jihar Barno domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti tare da dakarun su dake bakin daga.
Zalika rundunar, ta bayyana shirin bude wasu manyan hanyoyi da aka rufe a Jihar Barno saboda rikicin kungiyar Boko Haram.

A zantawarsa da sashin Hausa na RFI, daraktan yada labaran rundunar Janar Sani Usman
Kukasheka yace, a halin da ake ciki rundunar sojin Najeriya ta kafa sansanoni 14 a cikin dajin Sambisa.
Kukasheka ya ce babban dalilin bawa manyan kwamdojin soji umarnin gudanar da bikin Kirsimeti a Borno, shi ne don karawa sojin da ke bakin daga kwarin gwiwa.
A gefe guda kuma, darakatan yada labaran rundunar sojin ya ce, a wani yanayi da ke nuna ingantar tsaro a yankunan da a baya ke fama da hare haren Boko Haram, za’a bude manyan hanyoyi guda biyu da aka rufe saboda rashin tsaro.
Hanya ta farko it ace wadda ta tashi daga garin Maiduguri zuwa Damasak, sai kuma wadda ta tashi daga Maiduguri zuwa garin Baga.
RFI HAUSA

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN