KANUN LABARAI DAGA JARIDU DA KAFOFIN LABARAI 18/12/2016

DW Hausa-Zaben 'yan majalisar dokoki a Cote d'Ivoir

 Awannan Lahadin ne'yan kasar Cote d'Ivoir fiye da miliyan shida ke zaben 'yan majalisun dokokin kasar 255. Da misalin karfe takwas ne dai agogon GMT aka buda runfunan zabe 19,800 a kasar.

Wannan zabe na a zaman na farko a karkashin sabuwar jamhuriya ta uku bayan zaben rabagardama da ya amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar a watan Oktoban da ya gabata.
A cewar hukumar zaben kasar ta CEI, za a rufe runfunan zaben ne da misalin karfe shida na yamma agogon GMT, sannan kuma sakamakon zaben zai iya kai wa ranar Laraba kafin a same shi, sai dai kuma ana iya samun sakamakon wuccin gadi kafin wannan rana.
Duk da ana cewa mata za su taka rawar gani a fagen siyasar kasar ta Cote d'Ivoir, amma kungiyar mata da ke fafutikar samun daidaito tsakanin maza da mata a kasar, na ganin cewa babu takarar mata da yawa a zaben, inda ta ce mata 43 ne kawai daga cikin 'yan takara 1,337 ke yin takarar.

BBC Hausa-Real Madrid ta lashe kofin duniya na zakarun nahiyoyi

Real Madrid ta ci kofin duniya na zakarun nahiyoyi, bayan da ta doke Kashima Antlers da ci 4-2 a fafatawar da suka yi a ranar Lahadi.
Real Madrid ta ci kwallon farko ta hannun Kareem Benzema a minti na tara da fara tamaula, sannan Cristiano Ronaldo ya kara ta biyu a bugun fenariti a minti na 60 ana murza-leda.
Ita kuwa Kashima Antlers ta fara cin kwallo ne ta hannun Gaku Shibasaki daf da za a je hutun rabin lokaci, kuma bayan da aka dawo ne daga hutun ya kara cin ta biyu.
Haka aka tashi wasa 2-2 daga nan ne ka yi karin lokaci na minti 30, wasan farko minti 15 ya sake fafatawa karo na biyu minti 15.
Nan ne fa Real Madrid ta samu damar kara cin kwallaye biyu ta hannun Cristiano Ronaldo, wanda hakan ya sa ta lashe kofin duniya na zakarun nahiyoyi.
Wannan ne karo na biyu da Madrid ta ci kofin bayan wanda ta dauka a 2014.

BBC Hausa-'Mun bai wa Majalisa mako biyu ta tabbatar da Magu'

Wasu 'yan Najeriya sun bai wa 'yan majalisar dattawan kasar wa'adin mako biyu da su tabbatar da Ibrahim Magu, a matsayin shugaban hukumar EFCC ko kuma su yi zanga-zanga a mazabun 'yan majalisar.
Sun bayyana hakan a wani taron manema labarai da suka gudanar a birnin Legas.
Sun kara da cewa duk wani yunkurin hana tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC na dindindin zai iya yin zagon-kasa a yakin da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi da cin hanci da rashawa.
A makon da ya gabata ne dai 'yan majalisar ta dattawan suka ki tabbatar da Magu a matsayin shugaban EFCC.
Sun ce sun yi hakan ne saboda rahoton sirri da suka samu a kansa na aikata ba daidai ba.
Sai dai shugaban na EFCC bai ce komai kan batun ba.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Mohammed Ali Ndume ya shaida wa BBC cewa sun mika wa Shugaba Buhari rahoton, yana mai cewa suna jiran matakin da zai dauka kafin su yi yunkuri na gaba a kan Ibrahim Magu.
Wasu dai na zargin cewa takun-sakar da ake yi tsakanin hukumar tsaro ta DSS da EFCC ce ta sanya manyan jam'ian na DSS suke yi wa Ibrahim Magu bi-ta-da-kulli, kodayake ba su ce komai a kan zargin ba.

DW Hausa-Dan kunar bakin wake ya halaka sojin Yemen 30

 sati guda bayan wani hari da kungiyar IS ta kai, inda ta kashe sojin kasar akalla 50.
Jami’ai a kasar sun ce sojojin sun yi layi ne domin karbar albashinsu a wata cibiyarsu da ke yankin Khor Maksar, dai dai lokacin ne kuma dan kunar bakin waken ya tada bam din da ke jikinsa.
A yanzu Aden shi ne babban birnin kasar Yemen na wucin gadi, da gwamnatin kasar da ta samu amincewar kasashen Duniya, kuma ta ke gudun hijira a Saudiyya ke daukarsa a matsayin fadarta.
Har yanzu dai gwamnatin Yemen na kokarin ganin ta mallaki cikakken ikon birnin, wanda har yanzu, yake fuskantar hare-hare.
Tun a watan Maris na shekarar 2015, Saudiya ke jagorantar rundunar sojin hadakar kasashen Larabawa da ke yakar ‘yan tawayen Houthi, bayan hambarar da gwamnatin kasar a waccan lokaci, sai dai kuma har yanzu an gaza korar ‘yan tawayen daga babban birnin Yemen wato Sanaa.dan kunar.

VOA Hausa-An Bukaci Buhari Ya Ziyarci Yankunan Da Boko Haram Ta Daidaita

Yayin da kwamitin gwamnatin tarayya da aka kafa domin farfado da yankin arewa maso gabashin Najeriya ya isa jihar Adamawa, al’umar yankin sun ce babbar bukatarsu ita ce a maido da matakan tsaro
A cewar wasu mazauna yankin Madagali akwai bukatar
jami’an tsaro da na kwastam da sauran hukumomi su koma yankin.
“Muna kira ga gwamanatin tarayya da a dawo da kananan ofisoshin ‘yan sanda da na kwastam da jami’an shige da fice da sauran ma’aikatan tarayya domin a samu mutanenmu su koma gida.” In ji Alhaji Muhammed Hassan, daya daga cikin matasan yankin.
Kwamitin ta da komadar yankin ya nuna damuwarsa mtauka kan yadda ya ga garin na Madagli, lura da yadda aka daidaita ababan more rayuwa da muhallan jama’a.
“Mun zagaya Madagali da Minchika, abubuwan da muka gani a Madagali kwarai ya tayar mana da hankali.” In ji Mista Adamu Kammale, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Madagali da Michika.
Ya kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya samu lokaci ya ziyarci yankin domin ya ganewa idonsa yadda al’amuran su ke.

Naij.com Hausa-Dambarwar siyasar jihar Ribas: Akwai yiwuwar PDP taji kunya

 Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan rikicin zaben jihar Rivers da ke kudancin kasar.
Kwamitin wanda ya kunshi kwararrun jami’an tsaro, zai zurfafaf bincike kan wani sakon murya da ake zargi ta Gwamna jihar ne Nyesom Wike, in aka ji yana yin bazarazar kashe jami’an hukumar zaben kasar, matukar suka gaza taimaka wa jam’iyyarsa ta PDP samun nasara a zaben na ‘yan majalisu.
An dai ji muryar na yin barazanar kisa ko kuma a dawo da cin hancin da aka bai wa jami’an INEC da ba a fadi sunayensu ba.
Sai dai ofishin gwamnan ya musanta zargin, yayin da ake sa ran fitar da sakamakon binciken nan da kwanaki 30, don bayyana shi ga jama'a.

Gida - Leadership Hausa

Assalamu alaikum, Editan LEADERSHIP Hausa mai farin jini, ka bani dama na yi kira ga gwamna Kashim...

Gida

(null)

Labarai, kai tsaye- Radio France Internationale RFI

Samu dukkanin shirye-shiryen RFI Siyasa da Al'adu da Wasanni da Labarai da dumi-duminsu na Afrika da Faransa da duniya.

NIGERIAN NEWSPAPERS

Flash or unlock your phone at SENIORA TECH shop No.51 upstairs.OLUMBO shopping complex Ahmadu Bello way Birnin kebbi. 08062543120 http://...

Wasanni

Domin samun labaran wasanni kai tsaye daga club na kwallon kafa na turai

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN