• Labaran yau

  HANYOYI 26 DOMIN ZAMA DA IYAYE LAFIYA NA 15 ZAI BAKA MAMAKI

  1. Ka ajiye wayarka yayin da Iyayenka suke yi maka magana. Kar ya zamanto suna yi maka magana, kai kuma kana danne-danne awayarka. (Browsing ko Chatting). Wannan Rainin wayo kenan.

  2. Ka rika neman shawara a wajensu. Kuma idan sun baka shawara ka rika dauka kana amfani da ita. Koda a kan neman aurenka ne- Girmamawa kenan.
  3. Kar ka rika tsoma baki acikin maganarsu, har sai idan sunyi maka izini. Kuma duk zancen da zakayi dasu, wajibi ne kayi amfani da zababbun kalmomi na Musamman.
  4. Koda an samu rashin fahimtar Juna a tsakaninka dasu, kar ka yarda su fahimci ranka ya baci, ballantana har ka furta musu wata mummunar kalma wacce zata Sosa musu rai.
  5. Ka rika yaba musu a bisa dukkan abinda su kayi maka komai kankantarsa. Koda addu’a sukayi maka, to lallai ka tsaya kayi musu godiya a bisa wannan.
  6. Ka rika girmama ‘Yan uwansu da abokansu. Ka rika ziyartarsu kana Kyautata alakarka dasu. Domin girmamasu kamar girmama Mahaifan naka ne.
  7. Duk lokacin da wani abin farin ciki ya sameka, To ka fara gaya ma Mahaifanka kafin ka gaya ma kowa. Amma idan abin bakin ciki ne, Kar ka yarda suji abinda hankalinsu zai tashi.
  8. Kar ka manta da Muhimman Gudunmuwar da Iyayenka suka bama rayuwarka. Ka rika ji a cikin ranka cewar babu abinda zaka yi ka iya biyansu.
  9. Wani lokacin zasu gaya maka labari kuma washegari su sake maimaita maka, sun manta cewa sun riga sun gaya maka. To amma duk da haka kar ka nuna musu kosawarka wajen sauraronsu.
  10. Abinda ya wuce ya riga ya wuce. Kar ka rika zargin iyayenka ko tuhumarsu da wani laifi. Kuma kar ka rika tuno musu wani mummunan labari.
  11. Kar ka rika shiga gaban Mahaifinka idan zaka yi tafiya. Kuma duk lokacin da kake zaune tare da shi a gida ko a Mota, Ka zauna cikin ladabi. Ka tashi tare da ladabi.
  12. Ka guji zagi ko bugun kannenka Ko Jikokin gidanku akan kananan abubuwa. Watakil yin hakan zai sosa zuciyar Mahaifanka.
  13. Ka rika amfani da Murya mai taushi, lafazi mai taushi, Kallo mai taushi a duk lokacin da kake tare da Mahaifanka. Kuma kar ka daga muryarka sama da tasu.
  14. Ka kiyaye Sirrin mahaifanka. Kar ka rika daukar labarin da zai janyo zubewar Mutuncinsu kana fadawa wa mutane.
  15. Mahaifanka sune abu mafi daraja, mafi tsada wanda ka mallaka. Don haka ka lailayesu, ka kula dasu fiye da yadda kake kulawa da kanka.
  16. In dai kana da hali, kar ka yarda kaci wani abu mai dadi ba tare da ka saya musu irinsa ko fiye dashi ba. Kar ka yarda kasha wani abu mai sanyi mai dadi wanda su basu sha irinsa ba.
  17. Ka kyautata musu suturar da suke sanyawa. Da kuma wajen kwanansu da abincinsu. Ka tabbatar ka ingantashi fiye da naka na kanka.
  18. Duk lokacin da basu da lafiya, Kar ka wakilta wani ya kula dasu. A’a kai ne zaka kula dasu. Ka kyale duk harkokinka. Kar ka manta lokacin da kayi zazzabi sanda kana yaro, ai ba su wakilta maka kowa ba. Su suka kula dakai.
  19. Kar ka rika jiran wai sai sun rokeka abu sannan kayi musu, a’a ka tabbatar kana yi musu tun kafin su nema.
  20. Idan kana zaune gida guda ko gari guda tare dasu, Kar ka yarda Safiya ta wuce baka je ka gaida su ba. Idan kuma kana aiki a wani garin ne, to koda duk Karshen mako ne, Sai kaje ka duba su Kuma ka nemi afuwarsu bisa rashin ganinka da ba su yi ba.
  21. Ka kasance ko yaushe cikin yin addu’a agaresu, ba wai sai a gurbin Sallah ba. Kuma ka rika neman afuwarsu da zarar ka fahimci wani abu ya sosa musu rai. Koda ba kai ne ka aikata ba.
  22. Idan kuma sun rasu, to kar ka dena addu’a a garesu har karshen rayuwarka. Kuma ka rungumi zumuncinsu ya zama naka.
  23. Ka rika shiga sha’anin kannenka da yayyenka gwargwadon yadda zaka kyautata alakarka da su. Kar ka rika nuna ‘Yan Ubanci ga wasu daga cikin kannenka. Yin hakan zai sosa zuciyar mahaifinka.
  24. Ka rika kiran mahaifanka da sunaye na girmamawa. Kar ka rika kiransu da sunayensu. Watakil yin hakan zai zubar da mutuncinsu a gaban mutane.
  25. Idan sun samu rashin fahimtar Juna a tsakanin junansu, Kayi kokari ka daidaita su ba tare da ka goyi bayan kowanne daga cikinsu ba.
  26. Ka kiyaye kar ka yarda ka fifita matarka akan iyayenka. Ana chanjin Mace, amma ba’a chanza iyaye.
  Ya Alah ka jikan Iyayenmu ka gafarta musu. Ka kyautata makwancinsu ka haskaka Kaburburansu. Kayi musu rahama kamar yadda suka ji kanmu tun muna kanana.
  Daga ZAUREN FIQHU
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: HANYOYI 26 DOMIN ZAMA DA IYAYE LAFIYA NA 15 ZAI BAKA MAMAKI Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });