• Labaran yau

  BARA A JININ HAUSAWA TAKE ?


  Almajirci a kasar Hausa daɗaɗɗan abu ne wanda aka saba yi, hasali ma saboda daɗewarsa ne wasu suke tunanin ko addini ne, amma dai zance mafi shahara ga gamsuwa shi ne al’ada ce.Iyaye kan dauki ‘ya’yansu wani sa’in har da na makota, a kai wani wurin malami da ke nesa da garinsu domin suyi karatun addinin musulunci, musamman ma Alkur’ani mai girma. Waɗanan yara sukan fara ne tun daga babba’u zuwa farfaru har cikin ikon Allah su sauke izu sittin kana su shiga neman ilimin sauran littafai, ana girmama su duk inda suka je, ta hanyar gaisuwa da ba su abinci kyauta ko kuma makwanci duk kyauta ba tare da tsangwama ballantana gori ba, yawanci zaka same su masu hankali, shiru-shiru da kumaladabi gami da biyayya.
  Wannan kaɗan kenan daga asalin yadda almajirci yake  a kasar Hausa a da. To amma shin haka abin yake a halin yanzu? Tambaya mai saukin amsawa, da nasan tabbas zaka iya amsa ta, to amma bari kaji yadda bincike ya nuna su wanene almajiran yanzu.
  Saɓanin da, almajiran yanzu, kaɗan ne suke da siffofin da na zayyana a baya, za ka same su da wasu ɗabi’o’i da kai ka rantse almajiri ba zai aikata ba.
  Sun fi son zuwa birni domin ya fi abubuwan more rayuwa.
  Wasu har a gidajen karuwai ake ganinsu suna aikace-aikace da yi mu su wankin rigar mama da ɗan tofi.
  Idan ka ba su abinci sai sun zaɓi kalar wanda za su ci, domin tuwo ya zama tsohon yayi.
  Kiriniya kuwa ko biri ya sallama su, ga wasan jaki da faɗa kamar dage.
  Kashi (ba haya) kuwa a cikin kwata da hanyar wucewa ba sai na faɗa maka ba, domin watakila kaima shaida ne.
  Kai wasu fa har halin ɓera suke, ‘yar wayar salula ko ‘yan sulallanka idan ka ajiye yanzu ka naima ka rasa, musamman a warin taro.
  Wannan kaɗanne daga halin al’majirin zamanin yau, amma fa ba duka haka suke ba, sai dai ɗan kuka shi yake jawa …
  To irin waɗannan halaye na su shi ne ya sa jama’a suka gaji da su gwamnati ta fara neman mafitar yadda zata warware wannan tsohon kulli.
  Tsohon Shugaban kasa Goodluck
  Ebele Jonathan ne ya fara fito da tsarin maganin bara ta almajirai a hukumance a matakin tarayya, amma sai dai kash shirin bai yi wani tasiri ba.
  Jihar Lagos ita ma tayi nata tsarin kuma sun sha kame da maido da duk wanda suka kama yana bara a birnin Jihar, amma abin takaicin shi ne Kano ce bolarsu ko kuma na ce a zatonsu duk ‘yan Kano ne mabaratan.
  To ba jimawa ita ma gwamnatin Jihar Kanon ta amince da dokar hana bara a mazanin tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, wanda wannan shi ya nuna cewa gwamnatoci a dukkan matakai sun kosa da wannan ɗabi’a ta bara.
  Ga dukkan alamu al’umma ne ba sa taɓuka wani abin a zo a gani wajen bayar da ta su gudummawar, mai baiwa tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau shawara kan harkokin tsangayu,
  Dr Bashir Shehu Galadanci, shi ne wanda a ya ɓullo da tsari a hukumance na fara shigo da al’umma cikin tsarin magance bara, bayan nan, shiru  kake ji kamar an aiki bawa garinsu.
  Bisa wannan dalili ne da ake ganin al’umma basa bayar da ta su gudummawar, kungiyar Hausawan Africa
  ta yunkuro domin samar da mafita ga matsalolin Hausawa,
  da kudirin Hausawa su magance matsalarsu da kansu. A zaman da ta saba yi a duk bayan mako biyu, kungiyar ta tattauna batutuwa da dama daga ciki har da wannan matsala ta bara, kasancewar Hausawa su ne da babban kaso a ciki.
  To za mu iya cewa kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu, domin kuwa yanzu haka kungiyar Gwadaben alkairi wadda guda ce daga cikin kungiyoyin da suke halartar taron Kungiyar Hausawan Africa, ta yunkuro gami da huɓɓasa wajen magance bara a yankinsu.
  Aminu Lawal  Salihu Garangamawa
  shi ne ya shaidawa Labarai24 a hirar da wakilinmu ya yi da shi, ya ce, bayan da suka koma gida ne suka nemi malaman al’majiran gami shaida musu aniyarsu ta samawa al’majiransu abinci ba tare da sun je bara ba, “nan take suka nuna amincewarsu da wannan tsari” sai dai Aminu Garangamawa ya ce halin matsin tattalin arzikin da ake ciki ne kawai ya sanya wasu masu hannu da shuni karɓar al’majiri ɗaya wasu kuma biyu.
  Daga bisani yayi kira da sauran kungiyoyi da su yi koyi da wannan abu da suka yi domin magance bara a kasar Hausawa baki ɗaya.
  Idan har kana biye da ni, ka ji cewa Gwamnati da al’ummar gari ba sa farin ciki da wannan aba da ta zamo alakakai a kasar Hausa wato bara, kuma da alama su kansu yaran da su ke yi ba a san ransu ba suke yi.
  Sai dai kash idan kowa ya gaji yaya har yanzu an kasa Kawo karshenta? Kodai bara a jinin Hausawa take? Kuma dai sun kasa gano sahihiyar hanyar magance ta ne?
  Tambayoyin da ya kamata Hausawa su amsawa kansu kenan a kan bara ta almajirci a kasar Hausa.
  Kana iya tura wannan rahoto ga duk wani Bahaushe domin ya san cewa akwai kalubale babba a gabansa, domin ana yi masa kallon mabaraci ne shi a sauran nahiyoyi. Kuma kana iya rubuto mana naka ra’ayin kan wannan batu ko kuma waninsa.
  Daga Abubakar SD

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: BARA A JININ HAUSAWA TAKE ? Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });