Sakamakon yawaitar karuwar yiwa mata
fyade da maza ke yiwa mata a Najeriya da ma duniya baki daya, ya zama
lallai mata su san abubuwan da ya kamata su yi idan a kayi rashin sa’a
ta gamu da ‘yan daukar amarya ko kuma wata’ yar uwarta mace aka yi mata
fyade,
to menene abinda ya kamata su fara yi?
to menene abinda ya kamata su fara yi?
Fyade na
janyo wata babbar damuwa ga gangar jiki da kuma dabi’ar wanda aka yiwa
fyaden ta hanyar damuwa da bakin ciki da tashin hankali da kuma
zurfaffen tunanin da ba na lafiya ba.
Amma fa abinda ya kamata wadanda aka yi
wa fyaden su gane shi ne yawanci ba laifinsu bane, saboda haka kar ki
dorawa kanki laifi ki na zargin kanki, maza karki kasa a gwuiwa wajen
neman magani da kuma shawarwarin likita.
Saboda haka ga wasu abubuwa 4 da ya
kamata kowacce mace ta sani domin daukar matakin gaggawa a duk sanda aka
samu faruwar wannan TA’ADDANCI a gare ta ko wata ‘yar uwarta mace.
1- GARZAYA KI NEMI MAFAKA
Abu na farko da ya makata ki yi shi ne ki
bar wurin da aka yi miki wannan ta’annati izuwa wurin da kika yarda
kika amince da shi nesa da inda abin ya faru. Walau gidan ‘yan uwanki ko
kuma gidan aminiyarki. Kada ki tsorata domin har yanzu kina raye kuma
ba kanki farau ba, a saboda haka kar ki ji kunya domin fyade ne aka yi
miki ba Zina kika yi ba, saboda haka karki ji kunyar tattaunawa da wanda
kika amince da shi sosai domin yin hakan zai taimaka wajen yarda da
aminci a zuciyarki da kuma wanda kika fadawa domin ya samu kwarin
gwuiwar baki shawarwari da kuma tausarki.
Akwai kungiyoyi masu zaman kansu wadanda
suke yaki da kuma kwato ‘yanci gami da tabbatar da adalci ga duk wacce
aka yi wa wannan aika-aika, kuma suna da kwararru da za’ a su baki
shawarwari a kan lafiyar ki.
2- GARZAYA ASIBITI DOMIN GWAJI
A asibiti ne kadai zaki samu cikakkiyar
kulawar kwararrun likitocin da suka kware a fannin maganin jima’i
wadanda za su auna ki domin fitar da rahotan da zai nuna zurfi da kuma
irin illar da kuma matakin fyaden wanda zai taimakawa ‘yan sanda wajen
bincike da kuma shaida a kotu.
Za’ a yi miki gwajin cuta mai karya
garkuwar jiki (HIV) da kuma sauran cututtukan da ake dauka yayin jima’i
(STD) da kuma gwajin juna biyu (Ciki) Tare da baki maganin daukar cikin,
domin kuwa shi la’anannen maras imanin da yayi fyaden watakila yana
dauke da cututtukan da sai an gwada za’a gani. ‘Yar uwa kada ki boye ko
kiji tsoro ballantana kunya domin in kinki zuwa dayan abubuwan da muka
fada na iya faruwa da ke.
A shawarce kada kiyi wanka,
kada ki canja kanyan jikinki, kada ki goge ko wanke farjinki ballantana
ki sha kowanne irin magani, za’a baki inda bukatar hakan a asibiti.
3- SHIGAR DA RAHOTO WURIN ‘YAN SANDA
Fyade babban laifi ne a dokar kasa wanda
bai kamata wanda yayi ya tafi a banza ba, ba tare da an hukunta shi ba,
don haka kada ki boye ta hanyar yin shiru, saboda haka maza ki garzaya
domin shigar da rahotan faruwar lamarin ga hukumar’ yan sanda domin bi
miki hakkinki, tabbata kin basu cikkken labarin yadda abin ya afku
domin su dauki jawabinki a rubuce wannan zai taimaka mutuka gaya wajen
bibo miki hakkinki.
4- NEMI SHAWARWARI
Fyade tun daga kalmar ma ba abu ne mai
dadi ba, a saboda haka duk wanda aka yi wa na iya fuskantar matsalar
damuwa da zurfaffen tunani wanda zai iya janyo mata doguwar matsala.
Wasu da aka yi wa fyade na iya cintar kansu a mummunan halin bakin ciki
gami da kunci (PTDS) tare da tsanar mutane musamman maza wanda wannan na
iya shafar yadda za suke tunani da kuma tafiyar da rayuwarsu, wannan
dalili ne yasa suke da bukatar shawarwarin kwararrun masana.
Ya
‘yar uwa ki yi hakuri, ki zamto mai karfin gwuiwa da kuma jajircewa
wajen bin hakkinki, ki dauka tamkar jarrabawa ce daga Allah kuma ki nemi
taimakonsa. Kada ki yi shiru wannan TA’ADDANCI ya tafi a banza, ke
kadai ce zaki iya fadar abinda ya faru a saboda haka kada kiyi kasa a
gwuiwa ballantana ki ji tsoro ko kunya.
Daga Abubakar SD.