• Labaran yau

  Tsakanin 'yan bangan vigilante da masu gyaran waya a Olumbo plaza

  Olumbo plaza,Birnin kebbi
  A ranar Littinin 26/9/2016 ne da misalin karfe biyu na rana rigima ya kasance tsakanin wata mata da ta kawo gyaran waya da shi mai gyaran,bayan da aka gano cewa screen na wayar ne ke da matsala sai aka karbi kudi N900 aka sayo screen aka sanya ma wayar,kuma wayar ta yi daidai kafin ta bar wajen mai gyaran a ranar Lahadi 25/9/2016.Washegari ran Littinin sai ta dawo akan cewa ai screen da ak sanya wa wayar jabu ne domin ya lalace,shi kuma mai gyara ya nace akan cewa ta dai yar da wayar,ko wayar ta fadi a hannun ta shi ya haifar da sake lalacewar screen din.Bayan ta wannan matar ta ci mutuncin wannan mai gyaran wayar ta hanyar gaya masa kalamai na cin zarafi,da barnar suna,cin mutuncin bai ishe ta ba sai ta je ofishin yan bangan vigilante wanda ke da ofis a bakin kasuwar Birnin kebbi,a inda tayi karar wannan mai gyaran inda aka hadota da jami'ai guda biyu ciki damara rike da kulki.
  Da suka iso wajen mai gyaran wayar sai suka yi bayani akan cewar wannan matar da suka zo da ita,ita ce tayi karan shi,mai gyaran ya dauko N900 da ta bayar da kuma wayar ta duk sai ya bata abin ta,sai amtar nan ta ce sauran kudin okada (kabu kabu) wada ta kashe wajen zuwa wajen shi da kuma su 'yan vigilante kudin zuwan su plazan da na komawar su duk da yake ita ta gayyato su wai sai a lissafa duk shi mai gyaran zai biya.Wanan al'amarin shi ya jawo hankalin mu inda muka zo muka tabbatar mata da rashin gaskiyar ta tunda an bata wayar ta da kuma kudin ta,a yayin nan su yan vigilante din sai suka tafi.Bayan kamar minti 30 sai wasu yan vigilante din kuma,daga ofis din su na bakin kasuwa sai suka zo,suka ce lallai za su tafi da shi tunda dai anyi karan shi,da na tambaye su a wane hurumi kuma ? tun da an bata wayar ta da kudinta ba bashi duk da haka za'a ja shi zuwa ofis wai ace me?.A nan muka lurar da su cewa tun da an bata wayar ta da kudin ta ai magana ya kamata ya mutu,amma inda suke shiga ba nan suke fita ba.
  Ina kira da babban murya ga kwamandodin vigilante na jihar kebbi,da cewa
  1.Wajibi ne ku dunke barakar da ke tsakanin ku,bangaren ofishin wajen skie Bank,da na bakin kasuwa da na GRA,saboda rarrabar ku shi ma barazana ne ga gudanar da ayyukkan ku da ingancin tsarin tsaro na sa kai.
  2.Ba zaku iya kare sunan vigilante ba idan daya daga cikin ku yayi kuskure,ko idan ya aikata laifi,dole ace dan vigilante ne tun da yana da kakin vigilante.
  3.Yana da kyau ku horar da jami'an ku game da tsarewa,da kare mutuncin 'yan jihar Kebbi wajen gudanar da ayyukkan ku ta hanyar gayyato masana su ba jami'an ku lakca game da hakan.
  4.Zai yi kyau ku ilmantar da jami'an ku kan hurumin gudanar da ayyukan ku,da kuma iyaka game da abin da ba hurumin ku ba,saboda yardar al'umma da imani da sukayi kan ayyukan ku shi ne nassara gareku,ba kame kame,ko tasa keyar mutum a gaba don wata bukata shine burgewa ba.
  5.Babban nassara a gareku shi ne saurin gano bata gari wayan da ke sanye da kakin ku,kuma suna jawo barnar suna gareku don ku gaggauta daukar nazartacce,da kuma ingantaccen mataki a kan su,domin ku tsabtace ayyukkan ku.

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Tsakanin 'yan bangan vigilante da masu gyaran waya a Olumbo plaza Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });