ISYAKU GARBA

Na buda wannan shafin ne domin samar da labarai musamman na Jihar Kebbi sakamakon rashin
wadatar Mawallafa da Marubuta masu zaman kansu wadanda suka sa dukiya da kuma lokacinsu domin samar da labarai na jihar Kebbi ta hanyar yanar gizo.Sa'ilin da labarai na gida jihar Kebbi basu samu ba sai mu samo labarai na Nishadantarwa kamar labaran al'ajabi wadanda su ne muka fi bayar da karfi akansu domin bincike da muka yi ya nuna cewa irin wadannan labaran jama'a suka fi karantawa.

Ni Isyaku Garba 'da ga tsohon Soja Marigayi Capt. Garba Tadurga asali 'dan kudancin jihar Kebbi ne daga Masarautar Zuru, tsohon jami'in hukumar tsaro na DSS, Marubuci, Masani harkar ingizon wayar salula da sadarwar zamani, Manazarci akan harkar tsaro kuma 'dan jaridar zamani na social Media.Na yi karatun harkar Jarida ta yanar gizo daga cibiyoyi da dama daga ciki har da Makarantar koyon aikin jarida na BBC wanda kyauta ne face lokaci da kake bukata da yanar gizo domin karanta darussa.

ISYAKU.COM yana da ma'aikata da ke aiki karkashinsa guda uku da wakilai hudu a fadin jihar Kebbi kawo yanzu.

Muna maraba da ku a ko da yaushe.
ISYAKU GARBA ISYAKU GARBA Reviewed by on December 16, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.