An fasa bawa Najeriya bashin da zata gina titin jirgin kasa


Mininstan Sufuri na kasa Rotimi Amaechi ya bayyana cewa matsalar kudi ce ta kawo tsaiko akan aikin ginin titin jirgin kasa wanda ya taso daga Ibadan zuwa Kaduna, duk da cewa akwai yarjejeniya da aka rattaba.

Amaechi wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Warri, ya ce aikin za ayi shi ne da bashin da aka karbo daga bankin Exim da ke China, amma kawo yanzu kudin bai zo ba, wanda hakan ya kawo tsaiko fara aikin.

“Mun sanya hannu a yarjejeniyar da za ta ba mu damar karbo rancen kudi kimanin sama da Dalar Amurka biliyan $6.7billion, wanda hakan zai bamu damar fara aikin gina titin jirgin kasan cikin kwanciyar hankali, Amma Bankin da zai bada wannan makudan kudaden wato Bankin Exim da ke kasar China, ya bukaci mu rage yawan kudaden" in ji Amaechi

Ya kara da cewa gwamnatinsu ta yi nasarar samar da kudin da aka yi titin dogo wanda ya tashi daga Itakpe zuwa Warri tare kuma da kammala aikin titin dogo daga Abuja zuwa Kaduna, wanda ya lashe zunzurutun kudi kimanin $1billion.

A karshe ya bayyana cewa kimanin mutane 150 aka dauka aiki bayan kammala aikin titin dogo wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, ya kuma ce wannan ba komai bane domin kuwa da zarar an kammala sauran layukan dogno, to babu shakka al'ummar kasar nan za su samu karin aikin yi.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN