Yadda wata Ma’aikata tayi facaka da Biliyan 5.7 wajen kallace-kallacen DSTV


Wani bincike da Ma’aikatar kwadago na Kasar nan ta soma ya nuna yadda wata Ma’aikata tayi facaka da mahaukatan kudi wajen kallon talabijin a tsakanin 2013 zuwa 2017. Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari ne tayi wannan bincike kwanan nan

Ministan Kwadago na Najeriya Chris Ngige ya sa ayi masa bincike kan zargin da ke yawo na cewa an yi faka da wasu kudi a Hukumar NSITF. Ana kishin-kishin din cewa Ma’aikatar ta kashe Biliyan 5.7 wajen ba Ma’aikata kudin kallon DSTV.

Ishaya Awotu wanda shi ne Shugaban kwamitin da aka nada yayi wannan bincike ya nuna yadda NSITF ta kashe wadannan makudan kudi wajen bada alawus na kallon tashoshi a talabijin. An ware wannan kudi ne ba tare da sa hannun Hukuma ba. Bayan nan dai Hukumar NSITF ta kasar ta warewa Ma’aikatan ta alawus iri-iri wadanda su ka hada da na kudin mota da na tufafi. An yi wannan aiki ne duk ba tare da sa hannun Hukumar da ke kula da albashi da alawus din Ma’aikatan Najeriya ba.

Hukumar NSITF ta kashe makudan kudi wajen wasu alawus ne dai da ba gane kan su ba. Binciken da aka yi ya nuna cewa ana fitar da kudi domin zuwa Kasashen waje yin kwas ba bisa ka'ida ba.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN