Wani 'Dan Fashi ya sace Motoci 32 cikin shekaru 2 a jihar Ondo


Mun samu rahoton cewa hukumar 'yan sanda reshen jihar Ondo ta dakume wani gawurtaccen dan fashi da ya yi kaurin suna tare da shahara akn satar Motoci. A yayin gabatar da wannan dan ta'adda, Olayemi Adeoye ga manema labarai a shelkwatar hukumar dake birnin Akure, kakakin ta Femi Joseph ya bayyana cewa, azal ce ta afka ma sa yayin da yayi yunkurin satar wata mota kirar Toyota Corolla mallakin wani mutum, Mista Olanipekun. Hukumar ta dakume Olayemi tare da abokin sana'ar sa, Waheed Anifowose, mai facin taya da ya saba kawo masu sayen motocin da zarar an sato su.

Olayemi mai sana'ar Walda da hukumar 'yan sanda ta dakume yayin satar motar mai lamba SS719 AAA ya bayyana cewa, ya na matukar samun annashuwa da farin ciki a duk sa'ilin da yayi satar mota musamman masu amfani da dan mabudi. Kakakin ya ci gaba da cewa, Olayemi ya shiga hannun hukumar ne inda aka sallame shi a ranar 15 ga watan Yunin da ya gabata kafin ta sake kai masa wawura a wannan lokaci.

Mista Femi ya kara da cewa, akwai sa hannun Olayemi a satar Motoci 32 cikin shekarun biyun da suka gabata, sai dai yana mamakin yadda yake kubuta daga dauri kuma ya sake komawa cikin al'umma inda yake ci gaba ta tafka ta'asar sa .
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN