Siyasar jihar Kebbi 2019: Ababe 3 da zasu iya zama barazana ga Gwamna Bagudu

Isyaku Garba | Birnin kebbi | 22-7-2018 |


Sannu a hankali 2019 ta gabato kuma kusan a ko'ina cikin fadin Najeriya duk wani dan siyasa ya fara binciken lafiyar motar da zai yi tafiya da ita a hanyar bulaguron neman mulki na siyasarsa. Hange da bicike kan yadda lamurran siyasa ke tafiya a jihar Kebbi, sakamakon haka ya nuna yadda jam'iyar APC ke iya fuskantar gagarumin cikas, matukar bata farga da wasu manyan damuwa da ke iya rikidewa zuwa babban matsala ba yayin da ta doshi 2019 domin ganin ta lashe zaben Gwamnan jihar Kebbi.

Bincike da isyaku.com ya gudanar, ya nuna cewa akwai manyan matsaloli guda uku da ke shirin yi wa jam'iyar APC barazana bisa tafiyarta zuwa 2019 a jihar Kebbi.

Na farko dai shine yadda wani dan takara Alh. Ibrahim Mera ya kunno kai daga Masarautar Argungu, sakamakon yadda dan takaran ya sami nassarar gamin gambiza tare da hadaka da wasu matasan kasar Masarautar Zuru da Yauri ya fara yin tasirin gaske, duba da yadda matasan na Zuru da Yauri suka yi na'am da manufofinsa cikin dan lokaci kalilan.

Na biyu kuma shi ne yadda wasu yan siyasar Masarautar Zuru suka dauki zafi, amma suka bar zancen a cikinsu. Sakamakon bincike da isyaku.com ya gudanar , ya nuna cewa shiru da wadannan yan siyasa suka yi, sun yi shi ne bisa wata manufa ta ramuwar gayya ta hanyar saka wa Kura da aniyarta a lokacin zaben 2019.

Wasu daga cikin dalilai da isyaku.com ya gano wanda su na cikin hujjoji da wasu jama'ar kasar Masarautar Zuru suke rike da shi , har da zancen yadda Mataimakin Gamnan jihar Kebbi Samaila Yombe Dabai ya aurar da 'ya'yansa mata guda biyu a lokaci daya cikin watan Disamban 2017 a garin Birnin kebbi. Yawancin jama'ar Zuru sun nuna bacin ransu tare da korafe korafe da dama a shafukan sada zumunta da wasu kafofin sadarwar zamani.

Amma rashin bayani akan dalili da ya sa shi yin haka ya harzuka wasu da dama da suke ganin a Zuru ne ya kamata a daura auren ganin cewa Masarautar Zuru ne yake wakilta a Gwamnatin jihar Kebbi, kuma ta hakan ne zai kawo martaba ga kasar Zuru domin ganin yadda jama'a daga wurare daban daban zasu halarci daurin auren.

Haka zalika, a cikin watan Maris 2018, Mataimakin Gwamna Samaila Yombe ya raba akalla motoci goma sha daya a cikin harabar gidansa na Gwamnati da ke GRA Birnin kebbi, wanda ya sa aka gayyato wadanda aka yi wa kyautar suka karbi motocin a gidan gwamnati a GRA Birni kebbi. Sakamakon haka wasu jama'r kasar Zuru da muka tattara bayani da korafe korafen su ya nuna yadda rinjaye a cikinsu suka nuna cewa hakan bai dace da girmansaba a matsayinsa na wakilin kasar Zuru a siyasar jihar Kebbi karkashin Gwamnatin Atiku Bagudu.

Wani jigo a siyasar kasar Zuru da baya son a ambaci sunansa a wannan rahotu, yace " Ni a nawa ra'ayi wannan babban kuskure ne Mataimakin Gwamna ya aikata a matsayinsa na shugaba kuma wakilin kasar Zuru a Gwamnatin jihar Kebbi, wai malam Isyaku bari in tambaye ka, kai kana cikin yan Jarida da suka watsa labari na bayar da kyautar wadannan  motoci,  to amma don Allah Isyaku manyan yan siyasa nawa ne ka gani a wajen wannan rabon motoci ?.

Kuma fa ana zancen siyasa ne fa ba wai wani ya yi nuni da alfahari da tunaninsa ba shi kadai, sha'anin siyasa jama'a ake nema, ko kuma a ja ra'ayin jama'a zuwa tsari da manufofinka, amma haka kawai mutum ya bushi iska ya dinga yin abu  shi kadai bai dace ba.

Abin da ya kamata a yi shi ne a gayyato jama'a yan siyasa maza da mata daga Masarautar Zuru da kuma wasu Masarautu, a yi kyakkyawar gangami a babban filin wasa na garin Zuru, garin Zuru ya dauki dan jama'a, a zo da motocin nan daga Birnin kebbi, a raba su a gaban daruruwan jama'ar kasar Zuru, wanda hakan zai zaburar da siyasar APC da jama'ar kasar Zuru ta hanyar karkato duk wata adamuwa zuwa kauna da yafiya amma ka gan ba'a yi haka ba."

Bisa wadannan hujjoji, har ila yau , isyaku.com ya gano cewa da dama daga cikin jama'ar Masarautar Zuru suna rike da wadannan ababe da wasu suka kira kurakurai, kuma fa matukar ba an bi da lallashi ba, sakamakon wannan fushi zai bayyana ne kawai a akwatunan zabe ko kuma ma wasu kan iya turjewa su koma wata jam'iya .

Na uku kuma shine ganin yadda yan takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP Atiku Abubakar, Sule Lamido da Kabiru Tanimu suka dau harama har ma sun kammala tsare-tsare da inganta Ofisoshinsu a garin Birnin kebbi, bayan duba da yadda wasu masu neman mukamin shugaban kasa a jam'iyar PDP suke ta neman hayan Ofishinsu a garin Birnin kebbi ya nuna cewa ashe fa har yanzu ba a kashe maciji ba. Duk da yake dubannin yan jam'iyar PDP sun koma APC ciki har da tsohon Gwamnan jihar Kebbi Sa'idu Dakingari, tsohon Minista Samaila Sambawa, tsohon shugaban jam'iyar PDP na jihar Kebbi Bello Doya da dai sauransu wadanda yanzu yan APC ne.

Ko ina aka kwana kenan a alkiblar siyasar jihar Kebbi ganin yadda wadannan ginshikan barazana suka kafu, kuma wasu jama'a suka rike su daram. Lokaci ne kadai ke iya fayyacewa ga mai karatu.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN