Sani Musa Saminaka | Shanga L.G| 16-7-2018
Ruwan sama tamkar da bakin kwarya ranar Lahadi ya yi sanadin cikewar Gulbin garin Saminaka, Wawa, Ganwo, Raha da kuma Dugu a yankin karamar hukumar Shanga na jihar Kebbi. Wannan lamarin ya yi sanadin shafewar gonakin gero, Masara, Dawa, Shinkafa da sauran amfanin gona sakamakon ruwa da ya mamaye gonakin.
Haka zalika wakilinmu na garin Saminaka ya tabbatar mana cewa hatta wasu gonakin Ayaba sun bi ruwa.
Wani dattijo mazauni garin Wawa, Malam Garba Layin Gehe, ya shaida mana cewa an taba samun irin wannan ibtila'i fiye da shekara goma da suka gabata a wannan gari.
Kawo yanzu dai babu labarin rushewar gidaje ko salwantar rayuwa, amma dimbin kayakin amfanin gona sun salwanta a wannan lamari.
Tags:
LABARI