Kebbi: Barnar ruwa a garin Alfagai, Yadda tawagar Alh. Abubakar Najakku suka jajenta wa al'umma

Isyaku Garba | Birnin kebbi | 3-7-2017 |


Rahamar ruwan sama kamar da bakin kwarya 'yan kwanaki da suka gabata, ya zama jarrabawa na ibtila'i ga al'ummar garin Alfagai da ke jihar Kebbi sakamakon ambaliyar ruwa da ya yi sanadin rushe wasu gidaje tare da mutuwar fiye da dabbobi 30, har da kayan abinci.

Bayanai sun ce ruwan wanda suka zo da tsakiyar dare sakamakon ruwan sama, sun malale wani bangare na garin na Alfagai babu zato ba tsammani.

Wakilin mu ya ga yadda ruwan suka yi barna, duk da yake babu rahotun salwantar rayuwa, amma an yi assarar dukiya mai dimbin yawa, musamman bisashe watau dabbobi, kayan abinci, gidaje wadanda gine ginen kasa ne.

Tawagar mai neman kujerar 'dan Majalisa na Birnin ,Kalgo, Bunza watau Alh. Abubakar Najakku sun sami isa garin na Alfagai karkashin jagorancin wani hadiminsa Hon Bello Sani, wanda ya zagaya garin na Alfagai, tare da yi ma al'ummar garin jaje a madadin Alh. Abubakar Najakku wanda bai sami zuwa ba a yau.

Hon. Bello ya jajenta wa jama'a kuma ya isar da sakon kunshi na wasika da Alh. Abubakar Na Jakku ya ba jama'ar garin Alfagai, wanda Sarkin Alfagai Alh. Musa Hashimu ya karba a madadin jama'ar garin na Alfagai. Haka zalika Sarkin ya yi godiya ga mai neman kujerar 'dan Majalisar cewa Allah ya biya masa bukatarsa.

Daga bisani tawagar ta dawo garin Makera, inda ruwa suka yi barna, nan cikin garin na Makera tawagar ta isar da sakon jaje tare da sako na kunshin wasika da Alh. Abubakar Najakku ya bayar wanda Kansila na ward, tare da wakilin Dan galadiman Makera suka karba.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN