Kara da EFCC ta shigar, Saidu Dakingari bai bayyana a Kotu ba sakamakon rashin lafiya

Isyaku Garba | Birnin kebbi | 2-7-2018


Wata babbar Kotun tarayya da ke garin Birnin kebbi ta ci gaba da sauraron kara da hukumar EFCC ta shigar a gabanta kan tsohon Gwamnan jihar Kebbi Sa'idu Dakingari tare da wasu mutun uku, bayan Lauyan EFCC ya bukaci Kotu ta bayar da izini domin a kamo tsohon Gwamnan ganin cewa wannan zaman Kotu shi ne na uku a jere, kuma Sa'idu Dakingari bai bayyana a gabanta ba a karo na uku.

Tun farko dai, Lauyan Dakingari Barr. Eyitayo, ya gabatar wa Kotu takardun Asibiti da ke nuni da cewa Dakingari baya da lafiya, kuma yanzu haka yana kasar Ingila. Ya kuma roki kada Kotu ta aika a kama shi, amma ya kara da cewa Dakingari zai bayyana a gaban wannan Kotu domin ya fuskanci tuhumar da EFCC ke yi masa.

Lauyan EFCC da Lauyan Dakingari sun gabatar wa Kotu hujjoji tare da shimfida madogarar hujjojinsu daga ayoyin doka na shari'a, inda Lauyan EFCC ya dage cewa Kotu ta bayar da warant a kamo Dakingari, a nasa cewa, a zaman Kotun a baya, Kotu ta ce za ta yi amfani da sashe na 394 CJA domin ta sa a kawo Dakingari a gabanta idan bai zo kotu ba ranar yau 2-7-2018.

Amm daga bisani Alkali Justice Simon Amobeda ya ce, duk da yake Kotu ta dau wannan niyyar a baya, amma yanzu haka an gabatar wa Kotu wasu sabbain bayanai da hujjoji da ya wajaba ta duba su, kuma Kotu ta yi haka ne domin a yi ma kowane bangare adalci.

Sakamakon haka, Alkalin Kotun ya ce, Dakingari 'dan adam ne kamar kowa wanda ke iya kamuwa da rashin lafiya a kowane lokaci, ya kara da cewa amma wannan lokaci shi ne zai zama karo na karshe domin a ba Dakingari dama ya kammala jinya.

Bisa wannan dalili ne Alkalin Kotun ya daga sauraron karar har zuwa ranar 24 ga watan Satumba 2018.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN