Kebbi: Karanta abin da Dan Bagudu ya yi domin wadata Yauri da wutan lantarki

Real Sani Twoeffect | Yawuri | 29-7-2018 |


Gwaunan Jahar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya samarda Taranfomomi Guda Uku (3) ga Al'ummar yankin Karamar Hukumar Mulki ta Yawuri dake Jahar  Kebbi.

Wannan yana daga cikin irin namijin kokarin da Gwamnan yake yi na ganin an wadata yankunan jahar baki daya da wutar lantarki

Sudai wadannan Taranfomomi guda uku za'a sakasu a unguwanni daban-daban dake yankin karamar hukumar ta Yawuri.

Da yake Jawabi,  shugaban karamar hukumar mulki ta Yawuri, Alhaji Musa Mohammed (Stone) yace:

"Gwaunatin Mai girma Gwaunan Jahar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu a shirye take wajen Samar da cigaban Jama'a a kowani lungu da sako na jahar, shiyasa a koda yaushe batayin kasa a guiwa wajen Samar da ababen more rayuwa ga Al'ummar jahar"

Ya kuma kara da cewa; "tabbas wasu yankuna na karamar hukumar suna cikin matukar bukatar Taranfomomin domin samun wadatacciyar wutar lantarki a yankunan, saboda haka ne Gwamnan Jahar bai yi kasa a guiwa ba wajen kawo dauki ga Al'ummar wadannan yankunan".

Haka zalika, shugaban karamar hukumar yace, wannnan abu da maigirma Gwamnan yayi ya cancanci a yaba masa matuka da gaske, saboda ya yi godiya ta musamman ga Gwamnan tare da kara mika kokon bararsa ga Gwamnan a kan sake samun wasu ayyukan na alheri a yankin.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN