An dakatar da ‘yan majalisar da suka yi yunkurin tsige gwamnan Benuwe


Majalisar dokokin jihar Benue ta dakatar da 'yan majalisunta takwas bisa yunkurin tsige gwamnan jihar Samuel Ortom.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa ‘yan majalisun wadanda ‘yan jam'iyyar APC ne sun shiga zauren majalisar ne domin kawo batun tsige gwamnan, a sanadin hakan ya janyo musu hukuncin dakatarwa har na tsawon watanni shida.

'Yan majalisun da ake zargi da aikata wannan laifi sun hada da; Adanyi Benjamin, Terhemba Chabo, Benjamin Nungwa, Bem Mngutyo, Adams Okloho, James Okefe da kuma Nick Eworo. ‘Yan majalisun sun samu jagorancin shugaban majalisar Terkimbi Ikyange, wanda tuni gwamnatin jihar ta dakatar da shi shima. Shi kuwa Gwamna Ortom, kamar yadda mai magana da yawunsa ya bayyana a cikin wani jawabi ya ce ‘yan majalisun basu da ikon tsige gwamnan saboda basu cika dokokin yin hakan ba. Ya kara da cewa ba su biyo hanyar da ta dace ba, ta yin amfani da kundin tsarin mulki ko kuma amfani da shari'a wajen aiwatar da kudurin nasu.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN