Shahararriyar mawakiyar kasar Colombia,Shakira ta watsa wa Yahudawan Isra'ila katsa ido don nuna goyon bayanta ga Falasdinawa.
Shakira
ta fasa yin shagalin da ta shirya yi a Tel Aviv, babban birnin kasar
Isra'ila,a ranar 9 ga watan Yulin bana, don yin Allah wadai da kisan
Falasdinawa.
Kungiyoyin
masu fafutukar share kwallan Falasdinawa da dama, sun aika wa
mashahuriyar mawakiyar goron gayyata don kakaba wa Isra'ila takunkumi a
fannin ilimi da raya al'adu,inda tuni ta yi maraba da yunkurinsu.
Shakira
wacce ta lashe lambar yabo ta Grammy,kana jakadar asusun kula da
kananan yara na Majalisar ta Dinkin Duniya, UNICEF,ta sanar da cewa,ta
fasa yin shagalin da ta shirya yi a Isra'ila,don yin Allah wadai da
kisan gillar da kasar Yahudu take ci gaba da yi wa al'umar Falasdinu.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
#TRT
Tags:
LABARI