NATO: Ba zamu tallafa wa Isra'ila ba, idan Iran ta kai ma ta hari

Sakataren janar na NATO, Stoltenberg ya sanar da cewa ba zasu taimaka wa Isra'ila,idan har maki babbar makiyiyarta,wato Iran ta kai ma ta farmaki.

Stoltenberg ya furta wannan kalamin gaban manema labarai kafar Associated Press (AP).

Haka zalika a ranar Asabar din ma,Stoltenberg ya maimata wannan furucin a jaridar Der Speigel ta kasar Jamus,inda ya ce,

"Isra'ila kawa ce ba mambar NATO ba.Babu wani tilashin bai Isra'ila kariya  kamar sauran kasashe.Kamata yayi mu nesanta kanmu daga duk wata matsalar da za ta gurgunta yunkurin samar zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da kuma guje wa haddasa fitintinu a Gabas ta tsakiya"
Wannan jawabin na sakataren janar na NATO ya zo daidai lokacin da Iran da Isra'ila ke ci gaba wasa wukake da harar juna.

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya soki yarjejeniyar nukiliyar da wasu kasashen Yamma suka kulla da shugabannin kasar Farisa.

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

#TRT 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN