May 17, 2018

Yadda Saraki ya sauka daga kujerarsa mataimakinsa ya dare domin bincike

Sakamakon takaddama da ta taso tsakanin safeto janar na 'yansanda da shugaban majalisar Dattawa ta Najeriya, dangane da zargin daure ma ta'addanci gindi a jihar Kwara, Sanata Bala Ibn Na'Allah ya gabatar da kudurin cewa shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki ya sauka daga kujerarsa na wucin gadi domin mataimakinsa ya dare saboda a sami nada kwamitin bincike da zai bincika zargin ba tare da nuna son kai ba.

Majalisar Dattawa ta aminta da haka bisa gaggarumin rinjaye kuma sakamakon haka Bukola Saraki ya sauka daga kujerarsa mataimakinsa ya dare.

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
Item Reviewed: Yadda Saraki ya sauka daga kujerarsa mataimakinsa ya dare domin bincike Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba

Raayin mai karatu

Koma Sama