May 15, 2018

Kalli yadda 'yan fashi suka yi ma wani soja - Munanan Hotuna

Wani soja ya rasa ransa bayan artabu da ya yi da wadansu da ake zaton 'yan fashi ne a karamar hukumar Keffi na jihar Nassarawa, sakamakon haka 'yan fashin sun harbe shi a fuska wanda ya haifar da mumunar rauni a barin fuskarsa na hagu.

Wasu bayin Allah sun garzaya da shi zuwa wani Assibiti inda aka dinke raunukan da harbin bindigar ya haifar a fuskarsa, amma daga bisani sojan ya rasa ransa,

Wannan soja ya biya babban farashi da ransa domin tabbatar da tsaron lafiyar jama'ar Najeriya kamar sauran soji.

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
Item Reviewed: Kalli yadda 'yan fashi suka yi ma wani soja - Munanan Hotuna Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba

Raayin mai karatu

Koma Sama