Yansanda sun kama mutum 12 dangane da fashi da makami na garin Offa

Yansanda sun cafke wadansu mutum 12 bisa zargin kasancewa da hannu a mumunar fashi da makami da aka yi a garin Offa na jihar Kwara ranar Alhamis da ya gabata.

Mai magana da yawun hukumar yansanda na Najeriya Jimoh Moshood ya yi bayani a kan lamarin tare da fitar da sunayen wadanda aka kama.

Wadanda aka kama bisa zargin kasancewa da hannu a fashin:

i) Adegoke Shogo 29yrs – An kama shi a Offa

ii) Kayode Opadokun 35yrs –An kama shi a Offa

iii) Kazeem Abdulrasheed 36yrs – An kama shi a Offa

iv) Azeez Abdullahi 27yrs – An kama shi a Offa

v) Alexander Reuben 39yrs – An kama shi ranar 11th Aprilu, 2018 a Lagos

vi) Jimoh Isa 28yrs – An kama shi ranar 11th April, 2018 a Lagos

vii) Azeez Salawudeen 20yrs – An kama shi a Offa tare da wayar salula da SIM na wadanda aka kashe a fashin.

viii) Adewale Popoola 22yrs – An kama shi a Offa tare da wayar salula da SIM na wadanda aka kashe a fashin.

ix) Adetoyese Muftau 23yrs – An kama shi a Ibadan na jihar Oyo

x) Aminu Ibrahim 18yrs – An kama shi a Illorin na jihar Kwara

xi) Richard Buba Terry 23yrs – An kama shi a Illorin na jihar Kwara

xii) Peter Jaba Kuunfa 25yrs – An kama shi a Illorin na jihar Kwara


Tuni dai sashen CIID na hukumar yansanda suka shiga aikin bincike gadan-gadan babu kama hannun yaro ganin irin aikin rashin imani da wadannan yan fashi suka aikata a lokacin farmaki a Bankin Union Bank na garin Offa.

Jimoh ya ce dukannin wadanda aka kama sun tabbatar ma yansanda cewa suna da hannu a wannan aika-aika.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Yansanda sun kama mutum 12 dangane da fashi da makami na garin Offa Yansanda sun kama mutum 12 dangane da fashi da makami na garin Offa Reviewed by on April 14, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.