April 26, 2018

Yadda wani mutum ke samun miliyoyin naira daga sana'ar kera bindigogi


Ibrahim Manu wani mutum ne mai shekara 50 da ya fada hannun yansanda bayan an kama shi yana kera bindigogi.Manu ya ce yana samun miliyoyin naira sakamakon kera bindigogin da yake yi a kauyen Beji da ke karamar hukumar Bosso a jihar Niger.

The Nation ta labarta cewa kera bindigogi gadon gidansu ne kuma shi bai san cewa haramtaccen sana'a bane.

Kakakin hukumar yansanda na jihar Niger Muhammed Abubakar ya ce an kama Manu da shaidar ababe da yake amfani da su domin kera bindigogin kuma rundunar yansanda za ta gurfanar da shi a gaban Kotu.

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
Item Reviewed: Yadda wani mutum ke samun miliyoyin naira daga sana'ar kera bindigogi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba

Raayin mai karatu

Koma Sama