Yadda janarori suka juya wa shugaba Buhari baya

Ga dukan alamu wadansu daga cikin tsofaffin janarorin soji ciki har da wadanda suka yi shugabancin kasar nan sun juya wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya tare da yunkurin ganin bai sake tsayawa takara a zaben badi ba, ko kuma idan ya tsaya za su yi duk abin da za su iya wajen ganin bai kai ga nasara ba.

Janar-Janar din da suka juya wa Shugaba Buhari bayan sun hada da Cif Olusegun Obasanjo, wanda a watannin baya ya fitar da wata doguwar wasika yana kira ga Shugaba Buhari cewa kada ya tsaya takara a zaben na badi

Obasanjo wanda ya ci gaba da caccakar gwamnatin Buhari a baya-bayan nan a duk inda ya samu kansa, yana zargin gwamnatin Buhari ne da gazawa a fannin tattalin arziki da kuma zargin Shugaban kasar da nada ‘danginsa’ a mukaman gwamnati tare da karkata harkokin tsaro kacokan ga Arewa.

Daga baya ma Obasanjo ya kafa wata kungiyar siyasa mai da’awar ceto Najeriya, wadda mutane da dama ke kallon ya kafa ta ce domin hada gangamin kawar da Buhari daga gadon mulki a zaben na badi.

Yayin da Obasanjo ke ci gaba da caccakar gwamnatin Buhari ne kwatsam sai Janar Theophilus Yakubu danjuma ya fito ya ce ’yan Najeriya su fito su kare rayukansu su daina dogaro da sojojin Najeriya, wadanda ya zarga da hada kai da Fulani makiyaya a jiharsa ta Taraba suna kashe kabilun yankin.

Janar danjuma ya ma yi gargadin cewa idan gwamnati ta gaza daukar mataki to abin da yake faruwa a kasar Somaliya zai zamo wasan yara idan aka kwatanta da abin da zai faru a Najeriya.

Ana cikin jimamin kalaman Janar danjuma ne, sai kuma Obasanjo ya sake shigowa fage, inda ya bukaci ’yan Najeriya cewa kada su yarda su sake zaben gwamnatin da ta gaza a zaben badi. Obasanjo ya ce “zai zama cikakkiyar wauta a ce ’yan Najeriya sun sake karfafa gazawa ta hanyar sake zaben gwamnatin da ta kasa yin katabus kuma gwamnatin da ta gaza a zaben 2019.”

Obasanjo wanda ya bukaci Shugaba Buhari da Jam’iyyar APC su daina bai wa ’yan Najeriya uzuri ya bayyana haka ne lokacin da wakilan kungiyar New Nigeria a karkashin jagorancin Chima Anyaso da Moses Siasia suka ziyarce shi a dakin Karatun Shugaban kasa da ke Abeokuta a ranar Litinin da ta gabata.

Kamar yadda ya fadi a wasikar da ya taba rubutawa Obasanjo ya zargi gwamnatin APC da “jawo kunci ga ’yan Najeriya” da “gudanar da tsarin tattalin arziki marar katabus” wanda ya ce ya “ruguza harkokin kasuwanci.”

Ya bayyana gwamnatin APC da “wadda ta gaza” kuma ya gargadi ’yan Najeriya cewa kada su sake zaben “kasasshiyar gwamnati da kullum ke neman uzuri kan gazawarta wajen cimma bukatun ’yan Najeriya.”

Sai dai kuma matsayin nasa bai bar Jam’iyyar PDP ba, inda ya ce kada ’yan Najeriya su rudu da neman gafara da PDP ta yi, inda ya ce PDP da APC, ba za su iya fitar da Najeriya daga tabarbarewar tattalin arziki ba.

Shi ma tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida ya bi sahun su Obasanjo, inda ya ce lokaci ya yi da tsofaffi za su mika harkokin mulki ga matasa su jagoranci kasar nan, inda ya ce, tsofaffin sun dade a harkokin mulki kuma tunaninsu irin na da ne.

Babangida ya bayyana haka ne lokacin da shugabannin kungiyar New Nigeria a karkashin Moses Siloko Siasia suka zaiyarce a gidansa da ke Minna.

Sai dai Janar Babangida ya nuna halinsa na Maradona, inda ya ki fitowa ya ambaci Shugaba Buhari kai-tsaye, amma ya ce: “Tarihi ya nuna cewa ci gaban kowace kasa ya fi gudana a hannun matasa da suke cike da sababbin dabaru. Wadansu daga cikinmu sun zama shugabanni suna da karancin shekaru. Tsofaffi nan ya kamata su ba da hanya ga matasa. Yanzu mun zama tsofaffin yayi yanzu lokaci ne na masu jini a jika, don haka a karfafa wa matasa su yi amfani da iliminsu na zamani don kai kasar nan gaba.”

Wata jaridar da ake bugawa a Intanet mai suna AljazirahNigeria ta ruwaito a ranar 2 ga Afrilun nan cewa, Janar T.Y. danjuma ya fara tuntubar Janar Obasanjo da Janar Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar da sauransu domin ganin Buhari bai kai labari ba a zaben na badi. Jaridar ta ce, a watan jiya ne Janar T. Y. danjuma ya fara wannan yunkuri lokacin da ya ziyarci tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bukaci su ajiye dukan sabanin da ke tsakaninsu don ceto kasar nan daga abin da ya kira kokarin rugujewa.

Wata majiya mai tushe kuma ta kusa da tsohon Mataimakin Shugaban kasar ta shaida wa AljazirahNigeria cewa: “T.Y. danjuma ne ya tsara ganawar. Kuma ya shaida wa Atiku cewa wajibi ne su yi aiki tare domin tabbatar da Shugaba Buhari da mutanensa ba su dawo kan gadon mulki ba.”  

Majiyar ta ruwaito Janar din yana cewa: “Wadannan mutane suna son ruguza kasar nan. Wajibi ne mu jingine dukan bambance-bambancenmu a gefe mu tabbatar ba su dawo gadon mulki a shekarar 2019 ba. kasar nan ta fada cikin rikici. Fulani makiyaya sun haukace, amma ba su cewa komai, kuma ba su yin komai. Idan kasar ta dare, ni da kai ne za mu fi shan wahala. Wadancan mutane ba su da abin da za su rasa. Ba su da wani kamfani a nan. Idan rikici ya balle, za su kwashe iyalansu ne kawai su gudu. Babu abin da za su yi asara. Mu ne manyan wadanda za su yi asara.”

Jaridar ta kara da cewa: “Tsohon Ministan Tsaron ya ce: “Yadda Fulani makiyaya suke dada baje kolinsu idan muka kyale su, kasar nan za ta kama da wuta. Don haka wajibi ne mu yi duk abin da ya wajaba don dinke kasar nan, hadin kan da sai mun yi aiki sosai kafin a cim masa da tabbatar da dorewarsa.”

Majiyar ta shaida wa jaridar cewa: “Janar (TY danjuma) daga nan ya je wurin IBB (tsohon Shugaban Soji Ibrahim Badamasi Babangida) da Abdulsalami (tsohon Shugaban Mulkin Soji Abdulsalami Abubakar) kan su taimaka wajen hado kan janarori domin su shawo kan Cif Olusegun Obasanjo ya mayar da wukarsa kube ta yadda dukansu za su tattaro jama’a su samar da dukiyar da za su mara wa Atiku Abubakar baya.”

Majiyar ta kara da cewa: “Janar danjuma ya kuma roki Atiku cewa zangon mulki daya kawai zai yi don mulki ya koma Kudu ta yadda mutanen Kudu ba za su ji a tauye su ba. Kuma ya ce wajibi ne su hada karfi da karfe wajen hade kan dukan shiyyoyin siyasa da kabilun kasar nan. ‘Ko a Arewa ba mu taba ganin irin wannan rarrabuwa ba,’ inji Janar danjuma. 
Sai dai a ranar Talatar da ta gabata, Kakakin Shugaba Buhari, Femi Adesina ya ce gwamnati ba za ta ce komai kan kalaman Cif Obasanjo game da gwamnatin Buhari ba.

A yayin da yake amsa tamayoyi a gidan talabijin na Channels, Femi Adesina ya ce, “Martanin da Ministan Labarai, Lai Mohammed, ya mayar wa Obasanjo a watannin baya, sun magance dukan zarge-zargen nasa na baya-bayan nan baki daya.”

Adesina ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta samu nasarar magance matsalolin kasar da suka shafi tattalin arzikin da tsaro, inda Najeriya ta samar da rara a asusunta na waje wadda ba a taba samun irinta ba a tarihin kasar. Don haka ya ce wannan suka ta Obasanjo ba za ta hana Gwamnatin APC ci gaba da bayyana wa ’yan Najeriya irin barnar da gwamnatin da ta shude ta tafka ba.

Sai dai a yayin da gwamnatin ta kauce wa mayar wa Obasanjo martani wani jigo a kungiyar Yarbawa ta Afenifere, Cif Ayo Adebanjo ya nuna kaduwa da caccakar da Obasanjo ya yi ga Shugaba Buhari a baya-bayan nan, inda ya ce, Obasanjo ba ya da mutuncin da zai iya zargin wani da gazawa.

Adebanjo wanda yake magana a wajen gabatar da littafin rayuwarsa mai suna “Tell it as it is- Fadi abin yadda yake,” a Legas a ranar Talatar da ta gabata ya bayyana tsohon Shugaban kasar da ‘Tauraruwa mai wutsiya.’

Cif Adebanjo ya ce, idan da Najeriya tana cike da mutane masu mutunci, mutane irin su Obasanjo ba za su sake iya shiga mutane ba, inda ya ce yana jin mamakin yadda mutane suke ci gaba da ba tsohon Shugaban kasa “martabar da ba ta kamata ba, lura da sanin halayensa.”

Ya ce yana da tabbacin cewa “Lokacin da gwamnatin talakawa ta gaskiya ta hau mulki, za ta kwace dakin Karatu na Shugaba Obasanjo da ke Abeokuta” daga tsohon Shugaban kasar. Adebanjo wanda zai cika shekara 90 a duniya a ranar 10 ga Afrilun nan, ya yi kaca-kaca da tsohon Shugaba kasa Obasanjo musamman a babi na 13 shafi na 233 mai taken:  ‘Awolowo, Obasanjo da kasar Yarbawa.’
Cif Ayo Adebanjo ya bayyana mulkin Cif Obasanjo da cewa shi ne mulki mafi zama annoba ga kasar nan.

Daga Aminiya

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com 
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN