Kotu ta bayar da belin Salman Khan kuma ya fita daga Kurkuku

Fitaccen Jarumin wasan finafinan Bollywood Salman Khan ya samu yanci bayan wata Kotun daukaka kara ta bayar da belinsa ranar Asabar.
Alkalin Kotun Ravindra Kumar Joshi ya bayar da belin Salman a kan Rupee 50.000 tare da samun wanda zai tsaya masa kafin ya bar Kurkukun da aka tsare shi a garin Jodhpur a yammacin India.

Bayan an sake Salman Khan nan take kide-kide raye-raye da bushe-bushe suka kaure a waje daga harabar Kotun wanda masoyansa suka yi ta shewa suna cewa "Muna kaunar ka ,kuma muna tare da kai Salman Khan!".

Bayan haka Salman ya zarce kai tsaye zuwa filin jirgin sama inda ya wuce zuwa garinsa na haihuwa Mumbai tare da kanwarsa Alvira da Arpita wadanda suke a cikin Kotun tsawon lokacin zaman ta.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Kotu ta bayar da belin Salman Khan kuma ya fita daga Kurkuku Kotu ta bayar da belin Salman Khan kuma ya fita daga Kurkuku Reviewed by on April 07, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.