Karanta dalili da ya sa aka yi ma wannan dansanda mugun duka a Lagos

Wani da ake zargin jami'in dansanda ne ya sha mugun duka a hannun wasu matasa da suka harzuka bayan dansandan ya harbe wani mutum a kai da bindiga sakamakon wani cacan baki a tsakaninsu a Mile 2 na garin Lagos.

Bayanai sun nuna cewa dansandan yana aiki ne a ofishin yansanda na Sagamu kuma lamarin ya faru ne bayan motarsa ta sami matsala sai ya tsaya a hanya, sakamakon haka wanda aka harba ya nemi bahasi da dansandan wanda ya harzuka matuka kuma daga bisani ya ciro bindiga Pistol ya harbi wannan mutum a kai.

Ganin haka ke da wuya su kuma matasa suka yanke masa nasu hukunci irin na yan bariki suka lafta mata dan karen duka, sakamakon haka suka yi masa jina-jina.

Amma bayanai sun ce DPO na Alapere mutum ne mai mutunci kuma sakamakon agaji na gaggawa da ya kawo nan take jama'a suka hakura.Yanzu haka wanda aka harba yana kwance a Asibiti rai a hannun Allah.


A post shared by kordaytyt (@koredespagetti) on
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Karanta dalili da ya sa aka yi ma wannan dansanda mugun duka a Lagos Karanta dalili da ya sa aka yi ma wannan dansanda mugun duka a Lagos Reviewed by on April 16, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.