Karamar hukumar Suru za ta fara ba matasa 1000 alawus na N5000 kowane wata

Shugaban karamar hukumar mulki ta Suru a jihar Kebbi Alh. Usman Maigandi ya ce karamar hukumar Suru za ta fara biyan matasa dubu daya 1000 alawus na naira dubu biyar N5000 kowane wata domin ta taimaka masu sakamakon rashin aiki.

Alh. Usman ya shai wa wakilin ofishin jakadancin Najeriya haka yayin da yake zanawa da shi ranar Talata a Suru.Ya ce wannan ya kunshi adadin Mata 400 da Maza 600 a fadin karamar hukumar mulki ta Suru.

Daga bisani ya kara da cewa Majalisar sa ta dauki nauyin biyan kudin magani ga musakai maras karfi a karamar hukumar.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Karamar hukumar Suru za ta fara ba matasa 1000 alawus na N5000 kowane wata Karamar hukumar Suru za ta fara ba matasa 1000 alawus na N5000 kowane wata Reviewed by on April 11, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.