Kalli bidiyon yadda aka yi fashi a Bankin Offa na jihar Kwara

Wani hoton bidiyo ya bayyana a shafukan yanar gizo daga na'urar CCTV na wani Banki wanda ake zargin ya nuna yadda yan fashi da makami suka yi fashi a Bankin da ke garin Offa na jihar Kwara ranar Alhamis da ya gabata.

A wannan hoton bidiyon an ga wata mata rike da yar karamar yarinya tana shiga Bankin yayin da wasu mutum biyu da ke tsaye a wajen ATM suka ruga da gudu bayan yan fashin sun fara harbin kan mai uwa da wabi daga wajen Bankin.

Rahotanni sun ce kimanin mutum 30 ne aka kashe a fashin da ya dauki awa biyu ana gudanarwa a garin na Offa ba tare da samun daukin gaggawa daga jami'an tsaro ba.Kimanin jami'an yansanda bakwai ne ake fargaban sun mutu a wannan fashi da makami na garin Offa.Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Kalli bidiyon yadda aka yi fashi a Bankin Offa na jihar Kwara Kalli bidiyon yadda aka yi fashi a Bankin Offa na jihar Kwara Reviewed by on April 11, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.