Ka san ko su waye suka fasa cikin wannan saurayi a Lagos ?

Wani babban kalubale da ke fuskantar al'umma shi ne yawaitar harkar shaye-shaye a tsakanin matasa, wannan saurayi ya gamu da ajalinsa ne a hannun wasu matasa da ake kyautata zaton cewa yan shaye-shaye ne wanda suka burma cikinsa da wuka a unguwar Aboye da ke Ejigbo a jihar Lagos.

PM News ta ruwaito cewa mazauna unguwar sun wayi gari ne suka gan gawar saurayin an burma cikinsa kuma sakamakon haka hanjin cikinsa suka fito yanayi da ya haifar da mutuwar saurayin.

Majiyar mu ta ce lamarin ya faru ne a wani sashe na Ejigbo wurin da aka shaida cewa matattara ce ta masu aikata laifuka wuri kuma da mugan mutane ke yawan ziyarta .

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Ka san ko su waye suka fasa cikin wannan saurayi a Lagos ? Ka san ko su waye suka  fasa cikin wannan saurayi a Lagos ? Reviewed by on April 11, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.