EFCC ta gurfanar da tsohon kakakin majalisar dokoki na jihar Taraba a Kotu

Hukumar EFCC reshen jihar Gombe ta gurfanar da tsohon Kakakin Majalisar Dokoki na jihar Taraba Honourable Mark Bako Useni, Hassan A Abubakar da John Danjuma Ali a gaban babban Kotun tarayya karkajin Justice Filibus Bitrus Andetur a Jalingo bisa zargin aikata ba daidai ba da dukiyar jama'a.

Hukumar ta yi zargin cewa Mark ya karbi N45m domin amfanin kansa yayin da Arc.Darius Ishaku tsohon dan takarar kujerar Gwamnan jihar taraba tare da John da Hassan suka karbi N267.46m daga badakalar kudi na  Diezani saboda a bayar da na goro ga jami'an INEC a jihar Taraba.

Bayan an karanta masu tuhumar da ake yi masu a gaban Kotu, dukan mutanen basu amsa laifin su ba sakamakon haka mai gabatar da kara Abubakar Aliyu ya bukaci Kotu ta sa rana domin a fara shari'ar.

Alkalin Kotun Justice Fibilus ya dage shari'ar zuwa ranar 26l,27 da 28 domin ci gaba da shari'ar ya kuma bayar da belin wadanda ake zargi.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN