April 30, 2018

Daukar cikin shege da mata ke yi ya sa an haramta ibadar dare a coci a Kenya

Hukumomi a gundumar Narok na birnin Nairobi a kasar Kenya sun bayar da umurnin haramta ibadar dare a Coci coci  sakamakon yawan cikin shege da yan mata ke yi.

Hukumomin sun ce bincike da aka gudanar ya nuna cewa rinjayen kananan yan mata da suka bakunci cikin shege sun dauki cikin ne ta hanyar fita da dare da niyyar zuwa Coci domin ibada.

Gidan talabijin na Citezen TV ya labarta cewa kwamishinan yansanda na gundumar Narok George Natembeya ya bayar da umurnin .

Ya kuma shaida wa mai gabatar da shirin cewa a watan Maris na 2018 yan mata 17 ne na makarantar sakandare a gundumar Narok suka dauki cikin shege sakamakon zuwa ibadar dare

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
Item Reviewed: Daukar cikin shege da mata ke yi ya sa an haramta ibadar dare a coci a Kenya Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba

Raayin mai karatu

Koma Sama