Rundunar ta kama wani mai suna Abu Alkali wanda ake wa inkiya da 'Wizi" a Unguwar-Dansanda a garin Bena da ke karamar hukumar mulki ta Danko/Wasagu wanda shi ne ke sayar da bindiga mai baki 2 (double barrel) akan N6.000 yayin da mai baki daya yana sayarwa akan N3.000.An kama shi da bindigogi daban-daban guda 11 a ranar 17 ga watan Fabrairu da misalin karfe 4:30 na yamma.
Amma a nashi jawabi Abu Alkali cewa yayi shi dan banga ne (Vigilante) kuma jama'arsa ce suka bukaci a sayo bindigogin a Mairairai, amma lokacin da ya kai yansanda wajen wanda yake kera bindigogin sun tarar cewa ya riga ya tsere.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Tags:
BIRNIN-KEBBI