Yan kungiyar asiri sun banka wuta a ofishin yansanda - Hotuna

Wasu wadanda ake zargin cewa yan kungiyar asiri ne sun yi wa wasu yansanda  mugun duka daga bisani suka banka wa ofishin yansanda na Oporama wuta a karamar hukumar Ijaw ta kudu a jihar Bayelsa ranar 21 ga watan Maris.

Majiyar mu ta ce wani dan kungiyar asiri da aka kama bisa zargin aikata mugan laifuka kuma aka tsare shi a caji ofis na yansanda a Oporama ya yi yunkurin tserewa ne shi kuma jami'in dansanda mai sintirin gadi ya harbe shi har lahira.


Sakamakon haka ya sa sauran yan kungiyar asiri suka yi gangami suka kai f
armaki a ofishin na yansanda kuma suka aikata wannan aika-aika.

Kakain hukumar yansanda na jihar Bayelsa Asinum Butswat ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce lamarin ya faru ne yayin da yansanda a Oporama ke shirye shiryen kai wanda ake tuhuma zuwa sashen SCIID a hedikwatar yansanda a Yenagoa.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Yan kungiyar asiri sun banka wuta a ofishin yansanda - Hotuna Yan kungiyar asiri sun banka wuta a ofishin yansanda - Hotuna Reviewed by on March 23, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.