Yan daba sun kashe wani jami'in dansanda a garin Lagos

Rundunar yansanda a jihar Lagos ta dukufa ka'in da na'in wajen neman wadanda suka kashe wani jami'in dansanda Sgt. Emmanuel Abam wanda ake kyautata zaton cewa zauna gari banza da ake kira area boys ne suka kashe shi a Akala Mushin a garin Lagos.

Kafin mutuwarsa, Sgt. Emmanuel yana aiki da rundunar yansanda shiyar D a Itire.

Tuni dai abokan aikin mamacin suka fara jaje a shafukan yanar gizo bisa kisan abokin aikin nasu.

Kawo yanzu dai hukumar yansanda na jihar Lagos bata fitar da wani jawabi ba akan wannan lamari kafin lokacin wallafa wannan labari.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Yan daba sun kashe wani jami'in dansanda a garin Lagos Yan daba sun kashe wani jami'in dansanda a garin Lagos Reviewed by on March 02, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.