Yadda mata ke dukan maza a gidajen aure a jihar Kebbi - CP Ibrahim Kabir

Kwamishinan yansanda na jihar Kebbi CP. Ibrahim Kabir ya ce yanzu haka rundunarsa ta sami rahotun karuwar yadda mata ke dukan mazajen su a gidajen aure a fadin jihar sabanin yadda aka saba gani na yadda maza ke ba matan su kashi a gidajen aure.

CP. Ibrahim Kabir ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake jawabi ga kungiyar National Council for Women Society na Najeria NCWS reshen jihar Kebbi  karkashin jagorancin Balkisu Atuna Danga wanda suka kai masa ziyarar aiki a ofishinsa da ke Gwadangaji ranar Talata.

Haka zalika Kwamishinan ya ce yan kwanaki da suka gabata rundunarsa ta sami rahotun cewa wani mutum ya caka wa matarsa wuka lamari da ya yi sanadin mutuwarta.

Ya kuma ce rundunar ta kama wani mutum wanda ake zargi cewa ya yi wa wata yarinya yar karama fyade a unguwar Badariya a mako da ya gabata kuma a cewarsa rundunarsa ta gurfanar da dukanin wadanda ake zargi a gaban Kotu kuma suna gidan Kurkuku bisa umarnin Alkalin Kotu yayin da ake ci gaba da shari'arsa a Kotu.

Daga Isyaku Garba

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Yadda mata ke dukan maza a gidajen aure a jihar Kebbi - CP Ibrahim Kabir Yadda mata ke dukan maza a gidajen aure a jihar Kebbi - CP Ibrahim Kabir Reviewed by on March 28, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.