Yadda aka yi da wadansu yan fashi kafin a kone su - Hotuna

Karya ta kare wai bori ya kashe Boka, domin jakar tamu ta magori ta yi burki a jihar Akwa Ibom inda ta dauko mana labarin wadansu matasa da suka gamu da ajalinsu bayan sun aikata fashi da makami kuma aka kama su a magamar Uyo-Itam a kan titin Calabar  zuwa Itu a birnin Uyo.

Wata majiya ta ce bayan matasan sun yi fashi ne sai aka bi su har jama'a suka kama su kuma suka zartar masu da hukuncin Kato na mai karfi ya bayar da umurni ko kuma kowa ma Alkali ne a lamarin, sakamakon haka aka kashe wadanda aka zarga da yin fashi kuma aka kone su nan take.

Bayanai sun ce daga bisani yansanda sun je wajen amma kafin su isa jama'a sun gama zartar tare da aiwatar da nasu hukunci inda aka bar gawakin suna suracin hayakin azabar babbaka daga wutar tayar mota.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Yadda aka yi da wadansu yan fashi kafin a kone su - Hotuna Yadda aka yi da wadansu yan fashi kafin a kone su - Hotuna Reviewed by on March 31, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.