Tsohuwa da ta bizine diya 7 daga cikin 8 da ta haifa bayan sun mutu

Allah sarki mai iko a kan komi, wannan wata tsohuwa ce da ta haifi yara 8 a rayuwarta amma kuma ta bizine 7 daga cikin su bayan sun mutu a lokaci dabandaban da kuma sanadi da suka banbanta . Yanzu haka wannan tsohuwar tana cikin wani yanayi mai ban tausayi ganin cewa diyarta ta karshe Ogechi Stella Njoku tana kwance a asibitin tarayya da ke Abuja.

Tsohuwa tana rokon Allah ya ba diyarta lafiya domin ya kasance diyar ce za ta bizine ta idan ta mutu ba wai ita tsohuwar ta bizine diya ta karshe cikin yara 8 da ta haifa a Duniya ba.

Yanzu dai haka diyar tana bukatar jinya na dialysis ne a Asibitin .

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Tsohuwa da ta bizine diya 7 daga cikin 8 da ta haifa bayan sun mutu Tsohuwa da ta bizine diya 7 daga cikin 8 da ta haifa bayan sun mutu Reviewed by on March 26, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.