Tsoho dan shekara 75 ya kashe kanshi domin matarsa tana bin maza

Wani tsoho dan shekara 75 mai suna Charles Okafor ya kashe kanshi domin matarshi ta ki ta daina yin zina a waje.

Sakamakon haka Okafor ya rataye kanshi har ya mutu a gidansa a jihar Anambra  inda aka ga gawarsa tana lilo da sanyin safiyar ranar 25 ga watan Maris.

Okafor dai uba ne ga yara 10 wanda ya gommace ya kashe kansa saboda bakin cikin abin da matarsa ke aikatawa na bin wasu maza a waje.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Tsoho dan shekara 75 ya kashe kanshi domin matarsa tana bin maza Tsoho dan shekara 75 ya kashe kanshi domin matarsa tana bin maza Reviewed by on March 28, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.