Saurayi ya yi wa mahaifiyarsa duka domin bata dafa abinci da yake so ba

Wani matashi dan sheakra 28 ya fada hannun hukuma bayan ya yi wa mahaifiyarsa duka domin bata saye masa wayar salula ba kuma bata dafa abincin da yake so ba. Alphonce Onyango yana fuskantar tuhumar duka tare da cin zarafin uwayensa laifi da ya aikata a rukunin gidaje na Umja a kasar Kenya.

Majiyar mu ta labarta mana cewa Alphonce ya dawo gida ne bayan ya yi tatil  da barasa kuma ya bukaci a ba shi wayar salula domin mahaifiyarsa ta ba kaninsa wayar salula.

Mahaiifiyarsa Josphine ta bukaci ya yi hakuri domin shi ya girma , wannan maganar ta harzuka Alphonce.

Daga bisani kuma ya bukaci a dafa masa wani nau'in abincinsu amma mahaifiyar ta ce ba irin wannan ne take dafawa ba sai ya yi hakuri ya ci wanda ake dafawa.

Sakamakon haka Alphonce ya yi barazanar cewa zai fesa majina a cikin abincin da ake dafawa wanda uwarsa ta hana, ana cikin haka ne sai mahaifinsa ya dawo nan take Alhonce ya rufe mahaifiyarsa da duka kuma yayin da mahaifinsa ya yi kokarin ya hana shi sai ya hada har da shi ya yi masu duka gaba daya.

Sakamako haka ya sa mahaifiyar Alphonce ta yi kara a wajen yansanda wadanda suka zo suka kama shi daga wajen da ya boye bayan ya tsere daga gidan.
 
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Saurayi ya yi wa mahaifiyarsa duka domin bata dafa abinci da yake so ba Saurayi ya yi wa mahaifiyarsa duka domin bata dafa abinci da yake so ba Reviewed by on March 20, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.