Matuka keke sun tube zindir domin nuna adawa da hadurra a Sao Paulo

Matuka kekuna da suka tube sun bazama a titin Sao Paulo na kasar Brazil domin nuna rashin amincewa da yadda hadarin mota ke kashe masu tuka kekuna a birnin na Sao Paulo.Dandalin Paulista a tsakiyar birnin Sao Paulo ya cika da Maza da Mata wadanda wasu suka tube zindir yayin da wasu suke sanye da dan bente kuma suna ta shewa suna ambaton kalamai da ke nuni da hukumomi su duba lamarin yawan hadurra da ke faruwa da masu tuka kekuna a birnin.

Wani bincike ya nuna cewa a 2017 mutum 37 sun rasu rayukansu sakamakon hadarin keke a birnin na Sao Paulo wanda shi ne birni mafi girma a kasar ta Brazil.

Haka zalika wani rahotu da International consultancy Inrix ta wallafa ya nuna cewa birnin Sao Paulo shi ne birni na hudu da ya fi hada hadar jama'a a Duniya bayan biranen Los Angeles, Moscow da New York.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Matuka keke sun tube zindir domin nuna adawa da hadurra a Sao Paulo Matuka keke sun tube zindir domin nuna adawa da hadurra a Sao Paulo Reviewed by on March 12, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.